Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami'in Hukumar Alhazai Ya Mayar Da Rarar Kudin Da Aka Ba Shi


Wadansu Mahajjata tsaye a wani sansanin alhazai
Wadansu Mahajjata tsaye a wani sansanin alhazai

Wani Jami’in hukumar jin dadin Alhazai ta jihar Neja, Nigeria ya mayar wa gwamnati tsabar kudi dalar Amurka dubu 20 da yace anyi mashi kari lokacin da aka bashi kudin guziri na Alhazan karamar hukumarsa.

Jami’in dai mai suna Muhammad Salish Abubakar mai kula da karamar hukumar Rijau a hukumar Alhazan, yace bayan ya rabawa Alhazan nashi kudin guzirini su 75, dalar Amurka 800 Sai yaga yana da rarar dala dubu 20 kimanin Naira Miliyan 8 na kudin Nigeria, Shine ya dawo da kudin a ofishin Hukumar Alhazan jihar ta Neja saboda a cewarsa ba hakkinsa bane.

Hukumar Alhazan jihar Nejan ta nuna jin dadi tare kuma da yaba wannan matakin ta kuma bashi takardar yabo ta Musamman kamar yadda Daraktan Ayyuka na hukumar Malam Attahiru Bala Dukku ya tabbatar,

A halin da ake ciki kuma, hukumar Alhazan Nigeria ta kai kara a kotu domin bin kadin mutuwar wani alhajin jihar da ya fado daga saman Na’urar kai mutane saman bene ya mutu a aikin hajjin da ya gabata bisa ga bayanin mukaddashin sakataren hukumar jin Dadin Alhazan jihar Neja Umar Makun Lapai.

Yanzu dai hukumar Alhazan tace ta bude kofar biyan kudin kujerar aikin Hajji mai zuwa da za a kai Naira Miliyan daya a Banki, ta kuma gargadi maniyyata kada su ba wani jami’in hukumar kudi a hannu.

Saurari cikakken rahoton Mustapha Nasiru Batsari.

Jami'in hukumar aikin haji ya mayar da rarar kudi-2:59"
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:59 0:00

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG