Kabilar kambari dake jihar Neja a Najeriya, ta gudanar da taronta na shekarar 2018 a kauyen Warari dake yankin karamar hukumar Rijau, inda taron yafi maida hankali akan sha’anin tsaro da kuma muhimmancin gudanar da babban zaben Najeriya na 2019 lafiya.
Shugaban kungiyar na kabilar Kambari a Najeriya Farfesa Muhammad Yakubu Auna ya ce ko bayan wannan ma suna gudanar da taron shekara ne domin bayyan muhimmancin hadin kai da kuma wayar da kan kabilar tasu wajan su tashi su bada gudunmuwa a harkokin siyasa.
Wasu daga cikin wadanda suka halarci taron sun bayyana muhimmancin sa ta fuskar hadin kai da wayar da kan mutanen karkara ta fannonin daban daban da kuma kiran gwamnati data kara kulawa da harkokin tsaro ganin yadda ya dagule a Najeriya.
Wakilin gwamnatin Jihar Neja a gurin taron Kwamishinan Shari’a, Barista Nasara Dan Malan ya ce gwamnati ta yaba da irin rawar da Kabilar Kambari take takawa wajan samar da zaman lafiya a tsakanin jama’a.
Saurari cikakken rahoton mustapha Nasiru Batsari
Facebook Forum