Makarantun da suka tsunduma yajin dai sun hada kwalejin kimiyya da fasaha da kwalejin horar da Malamai da kwalejin koyon aikin Noma da kuma kwalejojin koyan aikin kiwon lafiya da dukkanin su mallakar Gwamnatin jihar Nejan ne.
Masu yajin dai sun ce gwamnati ta gaza wajan cika alkawuran samar da kayan aiki a makarantun da kuma gyara azuzuwa a makarantun. Sannan suna neman gwamnati ta kyautata albashinsu.
Shugaban kungiyar ma’aikata da malaman makarantun gaba da sakandiren jihar Nejan Malam Adamu Zakari yace sune na baya a tsakanin takwarorinsu na sauran jihohi, kuma yajin na har sai abinda hali yayine.
Kungiyar kwadagon jihar Nejan tace ta goyi bayan matakin yajin aikin malaman kamar yadda shugaban kwadagon jihar kwamared Yahaya idris Ndako ya tabbatar, sai dai babban sakatare a ma’aikatar kula da ilimi mai zurfi a jihar Nejan Alh.Yakubu Muhammad Bello yace suna kokarin shawo kan matsalolin da suka addabi manyan makarantun jihar, ya kuma bayyana cewa, gwamnatin jihar tana neman hanyar da zata sasanta da malaman su koma bakin aiki.
Saurari cikakken rahoton Mustapha Nasiru Batsari
Facebook Forum