A karamar hukumar Wushishi ta jihar Neja ne daruruwan masu zanga-zanga suka fito tare da rufe babbar hanyar mota da ta hada Minna da wasu sauran garuruwa.
Al’amarin dai ya sa harkokin zirga-zirga sun tsaya cik har kimanin sa’o’i hudu zuwa biyar a yankin, haka kuma matafiya sun shiga cikin halin tsaiko.
Masu zanga-zangar sunce sun dauki wannan mataki ne domin nunawa hukumomi takaicinsu akan rashin samun wutar lantarki a kusan ilahirin karamar hukumar Wushishi.
Daya daga cikin jagororin masu zanga-zangar, kuma shugaban kungiyar ma’aikatan karamar hukumar Wushishi, Alhaji Mu’azu Sani, ya ce matsalar wutar lantanki ta addabesu inda har sun tuntubi hukumomin dake kula da wutar amma har yanzu babu labari.
Duk da yake Muryar Amurka ta yi kokarin jin ta bakin kamfanin dake samar da wutar lantarki shiyyar Abuja lamarin ya ci tura. Sai kuma gwamnatin jihar Neja ta ce tana kokarin shawo kan matsalar rashin wutar, kamar yadda kakakin gwamnan jihar Jibrin Baba.
Domin karin bayani saurari rahotan Mustapha Nasiru Batsari.
Facebook Forum