Kungiyar Miyatti Allah ta kaddamar da wani shiri na musamman da zai mayar da hankali kan wayarwa matasan Fulani kai, kan illar shan miyagun kwayoyi da kuma shiga bangar siyasa.
Da yake kaddamar da shirin a Minna, shugaban kungiyar Miyatti Allah, Alhaji Muhammadu Kiruwa Hardon Zuru, ya ce ya zama tilas su dauki wannan mataki, musamman a dai dai wannan lokaci na shiga hada-hadar siyasa a Najeriya.
Gwamnatin jihar Neja ta yaba da wannan mataki na fadakar da matasan Fulanin da kungiyar ta Miyetti Allah ta dauka. Babban darakta mai kula da harkokin makiyaya a ofishin gwamna, Alhaji Abdullahi Babaye, ya yabawa shugaban kungiyar Miyetti Allah da ya fara gudanar da wannan shirin a jihar Neja.
Yanzu haka kuma kungiyar Fulanin ta fara fadakar da makiyayan muhimmancin tsarin kiwo irin na zamani da zai kawo karshen al’adar zuwa kiwo kasa da kasa, da fulanin ke yi a halin yanzu.
Domin karin bayani saurari rahotan Mustapha Nasiru Batsari.
Facebook Forum