Kafofin Sadarwa na zamani ne dai suka fara yayata labarin wannan aure da suka ce yarinyar yar shekaru 15 ce. Sai dai iyayen yarinyar sunce shekarunta 20 da watanni 11.
A cikin hirarta da Sashen Hausa,Barista Maryam Kolo, shugabar hukumar kare hakkin Mata da yara kanana a jihar Neja, tace sun samu labarin auren kuma suna gudanar da bincike akan lamarin. Ta kuma yi alkawari cewa zasu dauki Matakin da ya kamata da zarar sun gano akwai Matsala a auren.
A nashi bayanin, dattijon ya bayyana cewa, abinda yafi damunshi shine, yadda ake yayata auren nashi a kafofin sadarwa da kuma bata mashi suna. Ya bayyana cewa, bai ga wani laifi ba a auren yarinyar kasancewa ba shi bane mijinta na farko, saboda haka baya ganinta a matsayin karamar yarinya duk da karancin shekarunta.
Babban wan yarinyar wanda ya bada aurenta bayan an biya sadakin Naira dubu dari uku ya tabbatar da cewa yarinyar ta haura shekaru 20 kuma kasancewa aurenta na uku kenan ba za a yi batun shekarunta ba, kuma ba a tirsasa mata ta auri dattijon ba.
Da yake tsokaci kan batun, babban daraktan ma’aikatar kula da harkokin addinai ta jihar Neja Dr. Umar Faruk Abdullahi yace auren bai sabawa shari’ar Musulunci ba.
Saurari cikakken rahoton:
Facebook Forum