A wata zantawa da Muryar Amurka ta yi da ambasada Ahmad Musa Ibeto, ya ce ya ajiye aikinsa ne don ra’ayin shiga harkokin siyasa, ganin yadda dokar ‘kasa ta bashi damar zaben duk wata jam’iyyar siyasa da yake ra’ayi.
Canza sheka daga jam’iyya mai mulki zuwa ta adawa da wasu manyan ‘ya ‘yan jam’iyyar APC su ka yi a baya-bayan nan, ya zamanto wani abu da ya dauki hankali kuma ba a saba gani ba a siyasar Najeriya.
Cikin manyan ‘yan siyasar da suka sauya sheka daga jam’iya mai mulki akwai shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki da kuma gwamnonin jihohin Benue da Kwara da kuma Sokoto.
Masana harkokin siyasa a Najeriya na ganin akwai matsala a wannan babban rashi da APC keyi a dai dai wannan lokaci da hada hadar siyasar kasar ke kawo jiki, sai dai shugabannin jam’iyyar na cewa babu komi, kamar yadda gwamnan jihar Neja Alhaji Abubakar Sani, ke cewa rashin da APC keyi bai damesu ba.
Domin karin bayani saurari rahotan Mustapha Nasiru.
Facebook Forum