Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Bukola Saraki ya amince zai amsa gayyatar da 'yan sanda suka yi masa domin ya wanke kansa bayan zargin da wasu 'yan fashi suka yi na cewa yaransa ne.
Sha’anin ayyukan kwamitocin ‘yan Majalisun Dokokin Najeriya ya shiga cikin jerin batutuwa dake janyo cece-kuce a tafiyar siyasar kasar.
Bayan lokaci mai tsawo da ta dauka tana mahawara akan amincewa da dokar kafa kungiyar zaman lafiya ta Peace Corps, Majalisar Wakilan Najeriya ta yi fatali da dokar gaba daya.
A yau ranar 14 ga Afrilu ne ‘yan matan da aka sace a garin Chibok na Jihar Borno, suka cika shekara hudu ba tare da ansan inda suke ba ko halin da suke ciki.
Kafafen yada labarai sun bada rahoton cewa wani jirgin kasa da ake kyautata zaton ya dauko wakilan, ya bar Beijing yau Talata da rana, kuma an dauki tsauraran matakan tsaro a birnin.
Kimanin watanni biyar ke nan da shugaban Najeriya ya gabatarwa da majalisun tarayya kasafin kudin 2018 wanda har yanzu majalisa ba ta zartas ba, ba abun da ya sa bangarorin biyu ke zargin juna da kawo jinkiri
Domin neman gyara tabarbarewar alamura a arewacin Najeriya inda babu tsaro, babu ilimi, babu tattalin arziki ingantace, matasa sun zama 'yan kwaya mata kuma sun sake suka sa 'yan siyasar yankin suka taru a Abuja domin yin gyara
Majalisar Dattawa da ta Wakilan Najeriya sun kafa kwamitoci biyu da zummar dakile yanyoyin dake jawowa gwamnati asarar kudi walao ta kayan da hukumar kwastan ke kamawa tana ajiyewa ne ko kuma hukumar gasa wadda ya kamata tana saka zunzurutun kudi cikin asusun gwmnati.
A bayan da gwamnan na Zamfara ya shaidawa majalisar dattawa cewa su na goyon bayan kafa 'yan sandan jihohi domin zai karfafa tsaro, sanata Mohammed Ubali Shittu da masu adawa da wannan sun ce Najeroiya ba ta haye matsalolin kabilanci da addini da zasu ba ta damar cin moriyar wannan ba
Kan majalisar dattijan Najeriya ya rabu gida biyu a bayan da shugaban majalisar, Bukola Saraki, ya tabbatar da rahoton amincewa da sauya jadawalin zaben 2019 wanda ya saba da wanda hukumar zabe ta gabatar
Kungiyoyin suka ce rikice-rikicen makiyaya da manoma da ake yayatawa, wani bangare ne na wani shirin neman gurgunta yankin arewacin Najeriya baki dayansa.
Wani sabon babi da aka bude dangane da makomar kananan hukumomi a Najeriya, ya haifar da sabuwar muhawara a tsakanin masu ruwa da tsaki a kasar da ma jama'ar kasar.
Yayin da wasu ke yabawa da irin wannan matakin,, wasu shugabannin nakasassu a Najeriya sun ce ganin kakar kyamfe na zabe yazo ne ya sa majalisar wakilai ke maganar ware musu kashi 20 cikin 100 na mukaman gwamnati.
Sai dai wasu 'yan majalisa sun ce sauya tsarin zaben da aka yi wata dabara ce ta neman tasirin siyasa ga wadanda ba zasu taka rawar gani ba a lokacin zaben.
A bayan wani taron da manyan hafsoshin sojan kasashen biyu suka yi a Maiduguri, manyan jami'an gwamnatin Najeriya da na Kamaru sun gana a Abuja
A Najeriya, an sake bankado wasu makudan kudade da yawansu ya kai Dalar Amurka miliyan 141, da aka boye a wani asusun bankin Keystone.
An gudanar da taro tsakanin gwamnatin Najeriya da kungiyoyin masu fafutukar kare hakkin yara daga kasashen waje da sauran masu ruwa da tsaki akan batun cin zarafin yara da a halin yanzu ya ke nema ya zama ruwan dare a Najeriyar.
Gwamnonin arewacin Najeriya sun nemi takwarorinsu na kudu maso gabashin Najeriya da su ja kunnen matasan yankunansu da ke kalamai masu haifar da rarrabuwar kawuna a Najeriya, musamman ma shugaban kungiyar IPOB Nnamdi Kanu.
Majalisar dattawan Najeriya ta yi wa kundin tsarin mulkin kasar gyara, kadan daga cikin abubuwan da aka yi wa kwaskwarima, akwai dokar da ta ba matasa damar tsayawa takara a matakai daban-daban ciki har da na mukamin shugaban kasa.
Hukumar zabe ta INEC a Najeriya ta dora alhakin dakatar da shirin kiranye da take kokarin gudanarwa a kan Sanata Dino Melaye da ke wakiltar mazabar Kogi ta yamma a kan kotu.
Domin Kari