Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Saraki Zai Amsa Gayyatar 'Yan Sanda


Bukola Saraki
Bukola Saraki

Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Bukola Saraki ya amince zai amsa gayyatar da 'yan sanda suka yi masa domin ya wanke kansa bayan zargin da wasu 'yan fashi suka yi na cewa yaransa ne.

A wata sanarwar da ya fitar, ya kara bayanin cewa gayyatar wani mataki ne na son bata masa suna. Saraki ya danganta wannan ne da takun sakar da ke faruwa tsakanin majalisar dattawan da sufeto janar na 'yan sanda, Ibrahim Idris wanda sau uku ya ki amsa gayyatar da majalisar ta yi masa a kwanakin baya, sai dai ya tura mukaddashinsa.

​Mene ne tanadin shari'a kan wannan gayyatar da ake yi wa shi shugaban majalisar dattawan?

Barista Mainasara Kogo Ibrahim ya mana karin haske inda ya ce kundin tsarin mulkin Najeriya da kuma dokar 'yan sandan kasar sun ba hukumar 'yan sanda ikon yin haka domin binciken laifin da ake zargin an aikata.

"Suna da hurumin da duk wani da akwai zargi akansa, wala'alla ana tunanin an aikata wani abu tare da shi ko kuma akwai wani abu da ya mallaka, ko kuma abu ya shafi ana binciken wasu kuma sun bada sunanshi, to akwai bukatar ya zo ko ba don komai ba domin ya wanke kanshi, ya kuma wanke kujerar alfarmar da ya ke zaune akanta." inji baristan

Haka zalika, ya kara da cewa a sashe na 26 na tsarin dimokradiyya, ko me aka zargin mutum da shi, yana nan ne a sunan zargi har sai abin da bincike na hukumomi ko kuma kotu suka tabbatar sannan za a san gaskiyar lamarin.

A ranar Lahadi ne 'yan sanda suka gayyaci shi Saraki zuwa ofishinsu na Guzape da ke Abuja, amma wasu na ganin wannan lamarin a matsayin bita da kulli.

"Muna bukatar sufeto janar na 'yan sanda ya tabbatar wa mutane cewar wannan magana da ya taso da ita yanzu ba bita da kulli ba ne. Saboda kowa ya san cewa majalisar ta sha kiransa ya bayyana gabanta amma ya ki. To menene tabbacin cewar wannan abu shi ma ba kirkirowa aka yi ba domin shi ma ya rama?" inji Kwamared Isa Tijjani

Ya kuma kara da cewa bai ga dalilin 'yan sanda na zuwa neman sahalewar Shugaba Buhari ba tunda ba wai an kira shi shugaban majalisar ba ne ya ki amsawa ba. 'Yan sanda hakkin bincike ne garesu amma hakkin tabbatar da mutum yayi laifi na ga kotu.

"Ya kamata su yi kokari su tabbatar mana da cewar abubuwannan da suke yi, suna yin shi bisa tsafta domin kada a je a jefa dimokradiyar tamu cikin rudanin da ba shikenan ba." inji Tijjani.

Saurari cikakken rohoton Medina Dauda

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:49 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG