An sami rahoton cewa wata tawagar manyan wakilan Koriya ta Arewa sun kai wata ziyara Beijing, abinda ke ruruta jita-jitan cewa shugaban Koriya Ta Arewa, Kim Jong Un ya gana da jami’an China a babban birnin kasar.
Jaridar Bloomberg, a wani rahoto ta fidda jiya litinin ya ambaci wasu majiyoyi guda 3 da ba a ambata ba, suna cewa shugaba Kim ya kai ziyarar bazata China. Kafafen yada labaran Koriya ta Kudu sun ce kanwar Kim ce ta jagoranci tawagar wakilan, ba shugaban ba.
Babu dai wata sanarwa a hukumance akan rahoton, wanda kafafen China da Koriya Ta Arewa basu ce komai akai ba. In rahoton ya tabbata, to wannan ne zai kasance karon farko da shugaba Kim zai kai ziyara a wata kasa tun bayan da ya fara mulki a shekarar 2011.
Facebook Forum