A bayan da shugaban kungiyar gwamnoni ta Najeriya, gwamna Abdul'aziz Yari na Jihar Zamfara, ya bayyana a gaban wani taron majalisar dattijai cewa su na goyon bayan batun kafa rundunar 'yan sandan jihohi dari bisa dari domin kawo karshen matsalolin tsaro a kasa, masu adawa da wannan batu sun fito su na yin tur da haka.
Daya daga cikinsu, shi ne Sanata Mohammed Ubali Shittu, wanda yace kafa rundunar 'yan sandan jihohi a Najeriya ba zai haifar da da mai ido ba. Sanatan yace, a halin da ake ciki a yanzu haka ma wasu jihohin ba su iya biyan albashin ma'aikatansu, ba su iya samar da kayan bukatu kamar ruwan sha da kiwon lafiya, sannan a ce za a dora musu nauyin aikin 'yan sanda.
Sanata Ubali Shittu, yace, "za a samu fitina a kasar nan, za a samu rashin kwanciyar hankali, domin kabilanci, bangaranci, bambancin addini da kabilu da suke fada da junansu zai kara yawa, kuma za a samu rashin fahimta."
Sai dai kuma mai magana da yawun majalisar dattijan Najeriya, Aliyu Sabbi Abdullahi, yana ganin lokaci yayi da ya kamata a ce Najeriya ta kafa 'yan sandan jihohi, domin a cewarsa, "ana samun matsalolin da kafin 'yan sanda su je wurin ana dadewa, sai an gama barna kafin mutane su samu agaji."
Yace da yake za a dauki mutane ne suyi aiki a yankunansu, zasu fi saurin zuwa, kuma zasu kasance sun san duk masu aikata irin wadannan laifuffuka a yankunansu.
Wani masanin harkar tsaro, kuma shugaban wani kamfanin tsaro, Kabiru Adamu, yayi kira ga hukumomin Najeriya da su yi taka tsantsan kan wannan batu domin harkar 'yan sanda tana tafiya da irin ingancin dimokuradiyyar da kasa take da ita.
Yace idan da a ce bangaren shari'a da na masu yind oka har da masu zartaswa su na da karfin da zasu iya taka ma gwamnonin jihohi burki, to ana iya tunanin kirkiro da 'yan sandan jihohi.
'Yan kasa da dama dai su na yin adawa da wannan shirin, akasari bisa dalilin cewa gwamnonin jihohi zasu iya amfani da su wajen cin zarafvin masu yin adawa da su, ko masu bambancin ra'ayin addini ko kabila.
Facebook Forum