Hukumar zabe ta INEC a Najeriya, ta kare kanta daga zargin da ake mata cewa ita ta dakatar da shirin yiwa Sanata Dino Melaye kiranye bayan da aka samu adadin mutanen da ake bukata kafin fara aiwatar da shirin, inda ta ce tana bin umurnin kotu ne.
A makon da ya gabata wata kotun tarayya a Abuja ta dakatar da shirin janye Melaye wanda ke wakiltar mazabar Kogi ta yamma.
“Akwai umurnin kotu da ya zo gaban hukumar zabe wanda ya ke nuni ga hukumar zabe cewa akwai magana da shi Dino Melaye ya sa a gaban wata kotu, don haka alkalin waccen kotu ya ba da takarda a kawo wa hukumar zabe.” In ji kakakin hukumar INEC Aliyu Bello.
Ya kuma kara da cewa, “ita kuma hukumar zabe a kullum tana mai biyayya ga dokokin kasa don haka wannan dalili na samun wannan takarda shine abinda hukumar zabe ta dogara da shi tun da ba za ta yi watsi da umurnin kotu ba.”
Hukumar zaben ta INEC ta kuma yi watsi da zargin cewa sun dakatar da shirin kiranyen ne saboda majalisar dattawan Najeriya ta yi barazanar gudanar da bincike a hukumar asusun tallafawa manyan makarantu ta TETFUND, inda shugaban INEC na yanzu Prof. Mahmood Yakubu ya taba aiki.
“Ko alama babu alakar waccan magana da wannan aiki, al’ada ce ga hukumar zabe a duk lokacin da ta samu umurnin kotu ta kan tsaya ta yi nazari ta ga me ya kamata ta yi.” Bello ya kare hukumar.
A baya jama’ar mazabar ta Melaye su 188, 580 ne suka sanya hannu domin yi mai kiranye, har kuma hukumar zabe ta fara tantance sunayen mutanen daga bisani kuma sai wannan umurnin kotun ya fito wanda ya nemi a dakatar da shirin.
Saurari rahoton wakiliyarmu Medina Dauda domin jin cikakken rahoto:
Facebook Forum