Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gamayyar Kare Muradun Arewa Ta Nemi A Kafa Dokar-Ta-Baci A Jihohin Da Ake Fitina


Matasan Arewa
Matasan Arewa

Kungiyoyin suka ce rikice-rikicen makiyaya da manoma da ake yayatawa, wani bangare ne na wani shirin neman gurgunta yankin arewacin Najeriya baki dayansa.

Gamayyar kungiyoyi masu rajin kare muradun yankin arewacin Najeriya, ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta dauki matakan kafa dokar-ta-baci a jihohin yankin dake fama da rikice-rikicen makiyaya da manoma.

A wurin wani taron da suka yi a Abuja, kungiyoyin sun bukaci da a cire shugabannin siyasa na wadannan jihohin daga kan kujerunsu har sai zuwa lokacin da aka samu maido da bin doka da oda.

Kungiyoyin suka ce wadannan fitinu da ake yayatawa, wani bangare ne na munafuncin da wasu ke kullawa da nufin gurgunta yankin arewacin Najeriya baki dayansa.

Jihohin da wadannan kungiyoyin suke son a kafa dokar-ta-baci sune Binuwai, Kaduna, Taraba da kuma Zamfara.

Jagoran wannan taron, Sharif Ashiru Nastura, yace idan ba yi hattara aka dauki matakan gaggawa ba, wannan fitina tana iya bazuwar da ba za a iya shawo kanta ba, musamman da yake batu ne da ya shafi addini da kabilanci.

Shugaban gamayyar ya tunatar da shugaba Muhammadu Buhari cewa ana neman kure hakurin mutanen Arewa, yadda kowace kabila ta bushi iska a Najeriya sai ta fito ta ce sai ta ga bayan Fulani ko sai ta gama da su.

Yace watakila shugaban yana dari-darin fitowa ya kare wannan cin zarafin da ake yi ma Fulanin ne domin kada a ce yana goyon bayan kabilarsa, amma kuma ai yayi rantsuwar cewa zai kare dukkan 'yan Najeriya, kuma su ma Fulanin 'yan Najeriya ne cikakku.

Sai dai kuma ministan matasa da wasanni na Najeriya, Barrister Solomon dalung, yace gwamnatin tarayya tana kan bakarta babu gudu babu ja da baya domin daukar matakan maido da zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Ya ce kalamun rura wutar fitina da kabilanci ba su da amfani a wannan lokaci.

Ita wannan gamayyar kungiyoyin kare muradun Arewa dai, ita ce ta janyo cece-kuce kwanakin baya a lokacin da ta bukaci 'yan kabilar Igbo da su bar arewa su koma yankunansu muddin su na da hankoron ballewa daga Najeriya don kafa kasar Biafra.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:11 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG