A wani mataki na kokarin rage hasarar da gwamnati keyi, majalisar dokokin Najeriya ta kafa wani kwamitin da zai toshe duk hanyoyin dake haddasa hasara domin gwamnati ta samu kudin shiga da zummar habaka tattalin arziki da inganta rayuwar al'umma.
Kwamitin zai nemi kawo karshen hasarar dubban miliyoyin Naira da ake yi ta hanyar barin kayayyakin da hukumar Kwastam take kwacewa su rube ko su lalace baki daya a wuraren da take tara irin wadannan kayayyakin da ta kama.
Sanata Dino Melaye shugaban kwamitin ya ce " Aiki aka samu kuma zamu yi aikin nan da tsoron Allah. Zamu yi aikin nan a cikin gaskiya." Sanata Melaye ya ci gaba da cewa zasu taimakawa Shugaban kasa wanda tuni ya bada umurnin a raba kayan abinci wa talakawa da wadanda karfinsu ya kasa. Saboda haka bai kamata a ci gaba da kulle kayan abinci a rumbun kwastam ba.
A can baya wasu rahotanni na cewa ita hukumar kwastam tana gwanjon kayan da suka hada da motoci ta yanar gizo. Akan haka ne wani tsohon dan majalisar wakilai ya yi tsokaci.
Malam Awalu Audu Gwadabe ya ce abun da kwastam keyi na kawo masu, musamman wannan gwamnatin, bakin jini a wurin jama'a. A cewarsa Shugaban kasa ya sa ido. Duk wanda aka kama kayansa kafin a yi gwanjo da kayan a neme shi. Sai a gaya masa kudin da aka yiwa kayan ya biya idan yana da kudi, idan kuma ba shi da kudin sai a sayar. Ya ce yin hakan shi ne adalci.
Muryar Amurka ta nemi taji ta bakin hukumar kwastam amma samun hakan ya ci tura.
Amma a nata yunkurin samarwa da gwamnti kudin shiga domin taimakawa tattalin arzikin kasa, majalisar wakilai ta kafa wani kwamitin da zai bi diddigin kudaden da hukumar kula da Gasar Tambola ta kasa, wato Lottery Commission, ke zuba wa a aljihun gwamnati. Dan majalisar wakilai Husseini Kangiwa shi ne shugaban kwamitin. A cewarsa duk kudin da hukumar ke biyan gwamnati bai wuce Nera miliyiyan dari bakwai ba. In ji shi idan har akwai kudaden da basu biya ba cikin shekaru goma sha daya za'a tilasta masu su biya.
Ga rahoton Medina Dauda da karin bayani
Facebook Forum