Rikici na neman kunno kai tsakanin sashen zartaswa da na majalisar dokoki akan kasafin kudin wannan shekara da shugaban kasa ya gabatarwa da majalisa kimanin watanni biyar da suka gabata.
Watanni biyar bayan an mika musu kasafin, yanzu sun fara zargin juna na kin tabbatar da kasafin.
Shugaban ofishin kasafin kudi Ben Nwabueze ya rabawa manema labarai wata takarda dauke da sa hanunsa inda ya karyata zargin da majalisar dokokin ta yi cewa hukumomi da ma'aikatun gwamnati ne ke jan kafa wajen ba da hadin kai domin a kammala aiki a kan shi.
Amma mai magana da yawun majalisar dattawa Sanata Aliyu Sabi Abdullahi ya ce " a lokacin da aka kawo inda an samu an yi aiki kashi hamsi sai kuma bayan wata uku an samu an yi wasu kashi 20 ko 30 mutane zasu gane ayyukan da aka yi" A cewar Sanata din ba'a yiwa masu neman ayyuka ba adalci, musamman wadanda suka kashe dukiyarsu suna neman ayyuka da aka riga aka tallata ma duniya.
Akan illar da wannan dogon jinkiri zai iya yiwa tattalin arzikin kasar masanin tattalin arziki Yushau Aliyu ya yi fashin baki. A cewarsa tattalin arziki zai shiga cikin wani rudani na rashin tabbas abun da kasafin ya kunsa. Zaaben da za'a yi shekara mai zuwa wanda aka riga aka fitar da jadawalinsa, zai kara dagula harkokin tattalin arzik.
Wasu 'yan Najeriya sun yi korafi akan rashin cika alkawuran da wannan gwamnatin ta yiwa jama'a Su 'yan majalisar ma tamkar suna yiwa kansu aiki ne, sun manta mutane ne suka zabesu su yi masu aiki.
Yanzu dai majalisar dattawa ta ba bangaren zartaswa ta kammala aikinta cikin mako daya , idan kuma ba haka ba majalisar zata dauki mataki.
Ga rahoton Medina Dauda da karin bayani
Facebook Forum