Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Takaddama Kan Shawarar Rushe Kananan Hukumomi a Najeriya


Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari

Wani sabon babi da aka bude dangane da makomar kananan hukumomi a Najeriya, ya haifar da sabuwar muhawara a tsakanin masu ruwa da tsaki a kasar da ma jama'ar kasar.

Kwamitin da Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya ta nada a karkashin Gwamnan Jihar Kaduna, Mallam Nasiru El-Rufa'I, domin ya kago hanyar da za a bi wajen gyaran fasalin kasar, ya mika rahoto inda ya ba da shawarar a rushe kananan hukumomi.

Wannan shawara ta gamu da fushin kungiyar ma'aikatan kananan hukumomi ta NULGE da ma wasu ‘yan kasa.

Shi dai rahoton ya ba da shawarar cewa a ruguje kananan hukumomin a hade muhimman ayyukan da suke yi da jihohi.

Sai dai tuni, wannan rahoto ya fara shan suka daga masu ruwa da tsaki a wannan fanni.

“Kwanan nan ake dawo da mutane daga Libya, sun je an mayar da su bayi, idan kananan hukumominsu suna aiki yadda ya kamata, wallahi babu matashin da zai bar kauyansu ya tafi Libya.” Inji Shugaban kungiyar ma’aikatan kananan hukumomi ta NULGE a Najeriya, Ibrahim Khalil.

Sai dai yayin da ake wannan takaddama, wasu na ganin bai wa kananan hukumomin ‘yancin cin gashi kansu shi ne mafita.

“Sai an ba kananan hukumomi ‘yancin cin gashin kansu, talaka ne ya zabi gwamnatin nan…. Ba fa mulkin soja mu ke yi ba.” Inji Nasiru Kabir, na kungiyar matasa ta Nigerian Youths for Positive Change da ke fafatukar neman sauyi na gari.

Sai dai dan majalisar wakilai, Muhamamd Musa Soba, ya ce, wannan batu na rushe kananan hukumomi shawara ce kawai kwamitin ya bayar.

“Wannan shawara ce kwamitin ya bayar, ba wai matsaya ba ce ta jam’iyar APC, ita kanta jam’iyyar sai ta zauna ta duba ta ga me ya kamata a yi.” A cewar Soba.

Batun kananan hukumomi a Najeriya, lamari ne da ke janyo zazzafar muhawara, domin kananan hukumomin, su ne rassasan gwamnati mafi kusa da jama'ar kasar.

Saurari rahoton Medina Dauda domin jin cikakken bayani kan wannan rahoto:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:48 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG