Majalisar Wakilan Najeriya ta fuskanci matsin lamba daga kungiyoyi masu zaman kansu, wadanda suka bayar da dalilan cewa kafa kungiyar zaman lafiya ta Peace Corps ka iya rage yawan matasan dake zama babu aikin yi, domin a cewarsu zai ‘kara inganta matakan tsaro da kasar ke bukata.
Ita dai wannan doka ta kafa kungiyar zaman lafiya ta Peace Corps, ita ce Shugaba Mohammadu Buhari ya ki sa hannu akan ta domin ta zama doka a bisa wasu dalilai.
A cewar Hon. Bashir Babale daga jihar Kano yayi jawabi a zauren Majalisa, inda ya ce duk duniya ana daukar kungiyoyin zaman lafiya a matsayin kungiyoyin sa kai, haka kuma bai kamata a goyi bayan kafata ba a Najeriya domin akwai ire-irensu dayawa a kasar.
Shi kuma Hon. Yusuf Bala Ikara cewa yayi kamata yayi a inganta abubuwan da aka san suna aiki, sai kuma a dauko wani sabo da zai zamanto aikin iri daya ne a kafa. Ya ce kamata yayi a gyara ayyukan ‘yan sanda da soja da jami’an tsaron farin kaya.
Domin karin bayani saurari cikakken rahotan Medina Dauda.
Facebook Forum