Shugabannin nakasassu a Najeriya su na bayyana ra'ayoyi kishiyoyin juna a dangane da wani shiri na ware kashi 20 cikin 100 na mukaman gwamnati a duk fadin Najeriya domin nakasassu.
Majalisar wakilai ta Najeriya, ita ce ta amince da ware wannan kaso na mukaman ga nakasassu, ganin cewa sun jima su na gwagwarmayar neman hakan.
Wakiliyar Muryar Amurka, Medina Dauda, ta ce shugaban Kungiyar Makafi ta Najeriya, Ali Yahaya Gwarzo, ya ce da gwaqmnatin Najeriya tana son yin dokar kyautatatawa nakasassu a kasar da tuni ta yi. Yace sun jima su na nema, har ma an watsa musu barkonon tsohuwa a majalisa don kawai sun fita neman wannan hakkin.
Yace a yanzu ma, an tado da wannan batun ne a saboda lokacin zabe yazo, su na bukatar kuri'un nakasassu da masu goyon bayan gwagwarmayarsu, amma da zarar zabe yazo ya tafi, shike nan haka za a watsar da maganar.
Amma shugaban Kungiyar Nakasassu Masu fama da Shan Inna, Misbahu Disi, cewa yayi wannan mataki na majalisar wakilan babban kalubale ne ga nakasassu a kan su tashi su nemi ilmi, domin kuwa idan ba su yi hakan ba, ko mukamai nawa aka ware musu, haka zasu gani su bari.
Yace wannan matakin ya nuna cewa gwamnatin yanzu ta saurari kukar da suka sha yi, tun ma kafin zuwanta.
Ali Sarkin Kutare na Abuja yayi kira ne ga jami'an gwamnati da su tuntube su, suyi musu bayanin wannan sabuwar doka, domin duk idan ba haka aka yi ba, to su kam ba su ma san da cewa an yi wannan dokar ba.
Wani dan majalisar wakilai mai wakilartar Pankshin, Timothy Simon, yace makasudin kafa wannan doka shine bayar da 'yanci ga nakasassu domin su san cewa kasa ta damu da su, kuma tana sane da su.
Facebook Forum