Gwamnan Jihar Neja Abubakar Sani Bello ya shugabanci kwamitin rikon kwarya na Jami'yyar APC a wurin karbar wani rahoto na musamman da Mataimakin Gwamnan Jihar Anambra ya mika wa Uwar Jam’iyya akan rabon mukaman shiyya shiyya.
Hukumar Alhazan Najeriya NAHCON ta umurci hukumomin alhazai na Jihohi su gaggauta fara shirye-shiryen aikin Hajjin bana.
Uwargidan Shugaban Najeriya Aisha Buhari, ta tofa albarkacin bakinta akan cece kuce da ke gudana a kasar sakamakon yin watsi da dokokin da ka iya ba mata damar samun kashi 35 cikin 100 na kujerun siyasa.
Cibiyar Kare Hakkin Masu amfani da wutar lantarki a Najeriya, ta aike wa Shugaban kasa Mohammadu Buhari takarda ta koke akan yadda kamfanonin wutan lantarki suke yawan dauke wuta, musamman a birnin tarayya Abuja.
Majalisar dokokin Najeriya ta gabatar da rahoton sassan da ta yi wa gyaran fuska a kundin tsarin mulkin kasar.
Majalisar Dokokin Kasa ta shirya wata doka da za ta sa ilimin aikin noma ya zama muhimmin darasi a manhajar makarantun sakandare a Najeriya, kamar yadda darasin lisafi da harshen turanci su ke.
A Najeriya, kwararru a fannin shari'a sun mayar da martani akan matakin da Majalisar Dattawa ta dauka na amincewa da kafa karin cibiyoyin horrar da lauyoyi 6 a kasar. A yayin da wasu ke yabawa da yin haka, wasu na cewa siyasa ce kawai.
Kwamitin da ke nazarin gyara kundin tsarin mulkin kasa na majalisar dokokin ya shirya taro da ya gayyato kakakin majalisun jihohin 36 saboda a samu amincewar majalisun dokokin a gyare gyare 51 da kwamitin ya riga ya yi a kundin tsarin mulkin kasar.
Kwamitin sulhu na 'ya'yan jam'iyyar APC da su ka samu sabani sanadiyyar zabukan gundumomi, kananan hukumomi da jihohi, ya bar baya da kura bayan mika rahotonsa ga shugabanin rikon jam'iyyar.
Majalisar Wakilan Najeriya ta kwaranye raderadin da aka yi cewa batun batar bindigogi dubu 178,459 a rundunar 'yan sanda zai wuce salun-alun.
A wannan karon an amince da zaben 'yar tinke, ko ta wakilan jam'iyyu ko ta sulhu amma akwai karin gyara da ya shafi kwarewar 'yan takara.
Wata tirka-tirka da ta kunno kai a kwanakin nan akan batun cire tallafin man fetur, ta sa kungiyar kwadago a Najeriya, zuburar da yan'uwan ta dake jihohi akan yin zanga-zangar lumana, daga ranar 27 ga wannan wata na Janairu da muke ciki.
Korafe-korafe sun kunno kai karara akan halin ko in kula da gwamnatin shugaba Mohammadu Buhari ta ke nunawa, musamman akan batutuwan iri su wa'adin shekaru na yin aiki, ko kuma wa'adin shekarun haihuwa na ma'aikaci da doka ko kundin tsarin mulki ya tanadar.
Mnistan yada labarai Lai Mohammed ya ce Twitter yana tara makudan kudade daga Najeriya ba tare da goyon bayan doka ko bin dokokin kasar ba.
Amma kwararru a fannin siyasa sun ce wannan abu ne mai kamar wuya duba da irin tuhume-tuhumen da ake yi wa Kanu.
Kwamitin kula da hukumar zabe a majalisar dattawa ya ce majalisar za ta yi zama na musamman akan dokar bayan ta dawo hutu.
Watanni uku kenan da jam'iyyar APC ta kafa kwamitin sulhunta 'ya'yan jam'iyyar masu korafi kan batutuwa daban-daban.
Tun shekaru biyu da suka wuce bayan Majalisa ta dawo da aiwatar da kasafin kudi daga watan Janairu zuwa Disamba, wannan shi ne karon farko da Shugaba Mohammadu Buhari ya yi zargin majalisar kasa ta yi cushe a kasafin kudin na shekara 2022 da ya riga ya rattaba wa hannu.
Domin Kari