A hirar shi da Muryar Amurka dangane da wannan zaman, Sanata Uba Sani ya ce wannan kundin tsarin mulkin ya dade ba a yi gyara ba, shi ya suka zauna da majalisar da dattawa da majilar dokokin don su tattauna domin a gyara don cimma matsaya daya. Dole sai da haddin kai kafin a samu gyara.
Ganin cewa gyaran kudin tsarin Mulkin ba zai yiwu ba, sai an samu kashi biyu bisa uku na Majalisun dokokin da na jihohi, kakakin Majalisar dokokinjJihar Neja Abdullahi Bawa Wuse ya ce dole ne a ba kowa dama ya baiyana ra'ayin sa.
A nashi bayanin, shugaban kwamitin duba kundin tsarin mulkin kasa kuma mataimakin shugaban majalisar dattawa Ovie Omo Agege ya yaba wa Ofishin raya kasa da Kungiyar Tarayyar Turai a bisa goyon bayan su wajen ganin an yi nasara a aikin gyare gyaren domin kyautata wa al'umman kasa.
Saurari cikaken rahoton cikin sauti: