Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Kwadago Za Ta Gudanar Da Zanga-zangar Lumana Kan Batun Tallafin Man Fetur


Shugaba Buhari da Kungiyar Kwadago
Shugaba Buhari da Kungiyar Kwadago

Wata tirka-tirka da ta kunno kai a kwanakin nan akan batun cire tallafin man fetur, ta sa kungiyar kwadago a Najeriya, zuburar da yan'uwan ta dake jihohi akan yin zanga-zangar lumana, daga ranar 27 ga wannan wata na Janairu da muke ciki.

Shugaban kungiyar kwadago Komred Ayuba Wabba ya ce duk wani yunkuri na cire tallafin man fetur a yanzu, alama ce na kin sauraren talakawa abinda kungiyar ba za ta lamunta ba.

Wabba ya ce kungiyar kwadago na adawa da shirin karin kudin man fetur ta bayan fage, saboda ha'inci da rugujewar siyasar karin farashin man fetur, da gwamnatocin da suka shude a Najeriya suka yi a baya, da kuma gazawar gwamnati mai ci yanzu wajen gyara matatun man kasar.

Wabba yayi karin haske akan shirin zanga-zangar, ya na mai cewa ba yajin aiki ne ba, za su yi zanga-zangar lumana ce saboda tattalin arzikin kasar na faduwa.

To sai dai a wani abu mai kaman mayar da martani, shugaban Majalisar Dattawa Ahmed Lawan ya fito fili ya kare wanan batu na cire tallafin man fetur, inda ya bada tabbaci cewa shugaban kasa bai shaida wa kowa cewa za a cire tallafin man fetur ba, kuma sun san cewa tallafin abu ne mai nauyi akan gwamnati.

Bincike ya nuna cewa tsakanin shekara 2012 zuwa yanzu an kashe kusan dalar Amurka biliyan 9.5 wajen gyara matatun man kasar, amma har yanzu shigo da tatatcen man fetur ake yi daga kasashen waje,

Saurari rahoton Medina Dauda cikin sauti:

Kungiyar Kwadago Za Ta Gudanar Da Zanga-zangar Lumana Kan Batun Tallafin Man Fetur
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:05 0:00


TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG