ABUJA, NIGERIA - Wannan ya biyo bayan wata takarda ta musamman da hukumar ta samu daga Masarautar Saudiyya dake nuni da cewa akwai yiwuwar za a bude kofofin Massallatan Harami guda biyu ga maniyyata daga sassa daban daban na duniya a bana domin gudanar da aikin Hajji.
Kafin a samu wannan sanarwar, an shafe shekaru biyu, Musulmin duniya ba su gudanar da aikin Hajji ba, sakamakon annobar coronavirus.
Wannan takarda ta sa hukumar alhazan kiran taron masu ruwa da tsaki domin yin bitar abin da takardar ta kunsa.
Wannan taro ya samu halartar Hukumomin alhazai na jihohi inda aka yi la'ákari da cewa akwai muhimmancin yin tsare-tsare na gudanar da aikin Hajjin bana, kamar yadda shugaban hukumar Alhazai Alhaji Zikirullahi Kunle Hassan ya bayyana wa manyan sakatarorin hukumomin jin dadin alhazai daga sassan kasar baki daya.
Zikirullahi ya ce akwai abin dubawa a yadda za a ayi shirye shiryen aikin Hajjin bana, ganin cewa abubuwa da dama sun sauya daga shekara 2019 da aka yi hajji zuwa yanzu. Saboda haka dole ne a yi musayar ra'ayi tsakanin hukumar alhazan da masu ruwa da tsaki.
Zikirullahi Kunke Hassan ya ce shirye shirye da wuri zai kawo masu saukin aikin, domin yanzu watakila za a rage yawan kujerun da za a ba kasashen da alhazan su za su yi aikin hajjin.
Saurari rahoto cikin sauti daga Medina Dauda: