Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Buhari Ya Zargi Majalisa Da Yin Cushe A Kasafin Kudin Shekara 2022 Da Ya Rattaba Hannu


Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari (Facebook/ Muhammadu Buhari)
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari (Facebook/ Muhammadu Buhari)

Tun shekaru biyu da suka wuce bayan Majalisa ta dawo da aiwatar da kasafin kudi daga watan Janairu zuwa Disamba, wannan shi ne karon farko da Shugaba Mohammadu Buhari ya yi zargin majalisar kasa ta yi cushe a kasafin kudin na shekara 2022 da ya riga ya rattaba wa hannu.

Sai dai Shugaban Majalisar Dattawa Ahmed Lawan ya ce ba cushe ba ne, yi wa al'umma aiki ne.

Shugaba Buhari ya rattaba hannu a kasafin kudin Shekara 2022, yin hakan na nufin cewa za a iya fara aiwatar da kasafin a wannan wata na Janairu.

Sai dai ya koka akan abin da ya kira cushe a kasafin, har na ayyuka 6,576 da Majalisar ta amince a cikin kasafin

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce bai ji dadin yadda Majalisar ta yi karin yawan kudin, wanda ake sa ran kashewa a kasafin kudin na bana ba, inda ya nuna cewa an kara naira biliyan 735.8 , ba tare da ba da wata hujja ba.

Ya ba da misalai na karin da aka yi a kudaden hukumomi da ma'aikatun Gwamnati da kuma na wasu kananan ayyuka.

Buhari ya kara da cewa zai aikawa Majalisa da wata takar da ta musamman akan karin da aka yi a kasafin bayan ta dawo daga hutu a karshen shekara.

Sai dai Shugaban Majalisar Dattawa Ahmed Lawan ya ce akwai kwararan dalilai da suka sa Majalisar ta yi kari a kasafin kudin daga Naira Triliyan 16.3 zuwa Triliyan 17.1 kuma sun kara kudin farashin gangar danyen man fetur daga dalar Amurka 57 da aka shimfida hasashen kasafin akai, zuwa dalar Amurka 62.

Sanata Lawan ya kara da cewa akwai manyan ayyuka da majalisar ta ke so a kammala kafin karshen wa'adin Gwamnati wanda shi ne ya sa aka yi karin.

A na shi nazarin, Kwararre a fannin tattalin arziki Shu'aibu Idris Mikati yana mai ganin ya kamata Majalisar ta rika sara tana duba bakin gatari.

Baya ga karin aiyyuka 6,576 da Majalisar ta yi a kasafin, an samu karin Naira biliyan 735.8 a yawan kudin wanda ya tashi daga Naira Triliyan 16.3 da Shugaba Buhari ya mika wa Majalisar , zuwa Naira Triliyan 17.1

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:07 0:00


Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG