Shugabancin rikon kwarya na Jam'iyyar APC ya yi Allah wadai da abin da ya bayyana a matsayin rahotannin karya da kafafen yada labarai na yanar gizo ke bazawa cewa an kori shugaban riko na jam’iyyar kuma Gwamnan Jihar Yobe Mai Mala Buni.
A wata ganawa da Gwamnan Jihar Neja, Abubakar Sani Bello, ya yi da Muryar Amurka, ya bayyana cewa labarin cire Mai Mala Buni ba gaskiya ba ne.
Baya ga wadannan bayanai na Gwamnan Jihar Neja, Abubakar Sani Bello, mai magana da yawun Jam'iyyar, Salisu Naínna Danbatta ya yi karin haske cewa Jam'iyyar APC tana nan a matsayin Jamiyyar siyasa mai cigaba da bin kaída domin ya zuwa wannan lokacin daukar wannan rahoto wani Kwamiti ne ya mika rahoto akan rarraba mukaman shiyya shiyya da Jam'iyyar ta kafa
Salisu Na’ínna Danbatta ya yi kira ga dimbin magoya bayan Jam'iyyar da su kwantar da hankalinsu, su mara wa Gwamna Mai Mala Buni baya ya gudanar da babban taron kasa da ya shirya a ranar 26 na wannan wata da muke ciki.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti: