WASHINGTON, DC - Amincewa da sabbin cibiyoyin ya biyo bayan wani rahoto da Ma'aikatar Shari'a, Yancin Bil’adama da Al’amurañ Shari'a ta fidda, na bukatar gyara dokar ilimin Shari'a ta shekara 2021 kuma Sanata mai wakiltar jihar Kogi ta yamma, Smart Adeyemi ne ya dauki nauyi kudurin.
Kafin wannan lokaci dai kasar ta na da cibiyoyin horar da lauyoyi guda 7, idan aka kara 6 zasu zama 13 kenan banda birnin tarrayya.
Ga Sanata Mai wakiltar Nasarawa ta yamma, Abdullahi Adamu wanda shi kansa lauya ne, ya yi na'am da wannan mataki da majalisa ta dauka duba da dubban dalibai lauyoyi da suke kammala karatun jami'o'i.
Shi ma Barista Dokta Mainasara Ibrahim Umar, ya na mai ra'ayin matakin zai iya kara karfafa fanin shari'a, amma da sauran rina a kaba. A cewar sa kamata ya yi a canza tsarin ilimin lauya ta yadda zai je daidai da tarihin kasar, da al’adu, zamantakewa da muradan al’umma.
Amma ga mai nazari a al'amuran yau da kullum, Abubakar Aliyu Umar, ya na ganin majalisar dattawa ta bar jaki ne ta na dukan taiki. Ya ce wannan wata hanya ce kawai ta yin wadaka da kudin gwamnati duba da babu wani kwakkwaran mataki da aka dauka akan matsalar tsaro da ta addabi makarantu a kasar.
Majalisar ta shawarci gwamnatin tarayya da ta bada fifiko wajen samar da isassun kayayyakin da za a yi amfani da su a cibiyoyin horar da lauyoyin domin inganta aikin doka a fadin kasar.
Saurari cikakken rahoton Medina Dauda.