Yanzu Majalisar ta cewa ba za a taba dokar ba sai bayan an dawo daga hutun karshen shekara a ranan 18 ga watan Janairun shekara 2022.
Majalisar dattawan Najeriya ta bi sahun majalisar wakilai wajen amicewa da kasafin kudin shekarar 2022 har da kari daga naira Triliyan 16.3 zuwa Triliyan 17.1.
Kungiyar Fulani ta Walidra da ke aikin wanzar da zaman lafiya a Najeriya ta koya wa mata fulani 200 sana'o'i hannu a Rugan Julie da ke karamar hukumar Karu ta Jihar Nasarawa domin taimaka masu su samu dogaro da kansu daga mawuyacin halin da yan bindiga suka jefa yawancin su a ciki.
Gamaiyyar Kungiyoyin Kwadago a Najeriya ta ce za ta yi iya kokarin ta wajen ganin ba a kara kudin man fetur ba.
Masu ruwa da tsaki a fannoni daban-daban na Najeriya sun kwashe kwanaki biyu suna tattauna makomar kasar a Abuja.
Tirka tirkar da ta faru har aka rasa wuta a babban birnin tarrayya da wasu Jihohi 5 a kwanakin baya ya fusatar da Kwamitin Kula da Bangaren Wutar Lantarki ta Majalisar Wakilai.
Majalisar Dattawan Najeriya na shirin kafa wata hukuma da za ta rika kula da bayanai ta kasa, wadda za ta daidaita ayukan hukumomi da suka dace.
Wasu Kwamitocin Majalisar Dattawa sun dauki lokaci su na tattaunawa akan batun daukar aiki a Ma'áikatu da hukumomin gwamnati har da bangaren Jamián tsaro, inda wasu suka nuna rashin gamsuwarsu da yadda ake daukan ma'áikatan Gwamnati da yadda ake maya gurbin jamián tsaro.
Gamayyar Kugiyoyin Mata Musulmi 21 a karkashin jagorancin Kungiyar Mata Musulmi ta Najeriya FOMWAN- ta yi kira ga Gwamnati Tarayya da kakkausar murya da ta samo hanya ta zahiri wajen magance matsalar tsaro da ta ki ci ta ki cinyewa a kasar.
Gwamnatin Najeriya ta ce za ta yi amfani da shawarar da Asusun Lamuni na IMF ta ba ta kan cire tallafin man fetur a watan fabrairu na shekara mai zuwa, sai dai da sharuda.
Bayan sauraren kokekoken tsoffin ma'aikata da suka aje aiki akan yadda suke samun matsala wajen karban hakkokin su, Majalisar Dattawa ta sha alwashin yin gyaran kudurin dokar fansho ta kasa domin anfanàr jami'an da suka aje aiki a kasa baki daya.
Daya daga cikin bayanan da Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Anthony Blinken yayi a ziyarar da ya kai Najeriya shi ne albishir da ya yi wa kasar na cire sunanta daga jerin kasashen da ke tauye 'yancin addini, batun da ya dauki hankalin al'umma.
Shugabancin Jamiyyar APC mai mulki ya kira taron majalisar dokokin kasa a Fadar Aso Rock kan za6en fidda gwani kai tsaye.
Babbar damuwar da ta kunno kai a zaben da APC ta yi a wasu jihohi ita ce, yadda aka samu bangarori biyu da ke ikirarin zama shugabannin jam'iyyar kamar yadda aka gani a jihar Kano.
Majalisar Dattawan Najeriya ta yi amai ta lashe dangane da sabuwar dokar za6e da ta yi wa gyara, yayinda ta amince Hukumar Za6e ta aika da sakamakon zabe ta hanyar da ta fi dacewa.
Kwamitin rikon kwarya na Jamiyyar APC karkashin gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni ya kaddamar da kwamitin sulhu na kasa gabanin babban taron jam'iyar na kasa da za a yi nan gaba kadan.
Ciyo bashin naira triliyon sama da 6 da za a yi kasafin kudin don rufe gibi, shi ne batun da ya fi daukan hankalin Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Ahmed Lawal.
A cewar masana tattalin arzikin kasar, wannan babbar nasara ce ga Najeriya duba da cewa za a samarwa matasa ayyukan yi.
Matafiya da ke bin hanyoyin sun ce masu motoci kan tafka asara ta rayuka da dukiyoyi saboda bacin hanyoyin.
Domin Kari