A sakamakon yin watsi da zaben shugaban Jam’iyyar APC ta Kano da kotun daukaka kara ta yi, bangaren Ibrahim Shekarau ya ce uwar Jam’iyya ta yi hanzarin mika takardar shaida ga Abdullahi Abbas domin za su daukaka kara zuwa Kotun Koli.
Wannan turka-turka ta samo asali ne daga zaben shugabanin Jamiyyar APC da aka gudanar a Kano ranar 18 ga watan Oktoban bara, inda aka samu rukuni biyu na shugabanin jam’iyyar APC a jihar.
Rukunin Gwamnan Jihar ta samar da Abdullahi Abbas a matsayin Shugaba, daya rukunin da ke karkashin tsohon Gwamnan jihar, Sanata Ibrahim Shekarau kuma ta samar da Haruna Danzago a matsayin na ta shugaban.
Ganin an samu shugabani biyu, sai bangaren Shekarau ya shigar da kara a kotun tarayya da ke Abuja wajen neman gane wane zabe ne sahihin zabe a jihar Kano a lokacin da aka yi zaben fitar da shugabani.
A ranar 30 ga wata Nuwamba na bara sai kotun tarayya ta yanke hukunci cewa zaben da bangare Shekarau suka yi shi ne sahihi, saboda haka Haruna Danzago shi ne shugaban Jam’iyyar APC a jihar Kano.
Akan haka ne bangaren Gwamna Ganduje ya kai kuka kotun tarrayya cewa su sake duba shari'ar amma aka fatattake su, ganin haka sai suka daukaka kara zuwa kotun daukaka kara ta Abuja inda ta yanke hukunci cewa Abdullahi Abbas na bangaren Ganduje shi ne zababben shugaban jamiyyar APC a Kano.
Sai dai Sanata Ibrahim Shekarau ya ce babu haufi, za su dakaka kara kan wannan hukunci da aka yanke.
“Abin mamaki yau, tsakanin yin hukuncin bai fi awa daya ko biyu ba, aka kira bangaren Ganduje, aka ba su takarda cewa su ne zababbu, wannan ya nuna mana cewa akwai ‘yan mowa da ‘yan bora a cikin jam’iyya.
“Mu mun yarda da matsayin kotu da hukuncin kotu, mu ba ma raina hukuncin kotu, mun karba, amma mun ba wa lauyoyinmu umarni da su yi nazari su tattara takardu domin mu je kotu ta gaba, wato kotun koli.” In ji Shekarau.
Amma sabon shugaban Jamiyyar APC a Kano Abdullahi Abbas wanda tuni har Uwar jamiyya ta riga ta bashi takardar shaidar amincewa da zaben sa, ya yaba da hukucin Kotun daukaka karar, yana cewa
“Ina so na yi Amfani da wannan dama na godewa Allah madaukakin sarki da ya kawo mu wannan lokaci, da wannan rana, ranar da kotu ta kara tabbatar da shugabancinmu Alhamdulillah mun godewa Allah.” In ji Abbas.
A yanzu dai yan kasa sun zuba ido su ga yadda wanan takkaddama za ta kawo karshe, ganin cewa saura kwanaki takwas kacal a gudanar da taron Jam’iyyar APC na kasa.
Saurari cikakken rahoton Medina Dauda daga Abuja: