Sassan da aka yi wa gyara sun kai 55 amma wadanda suka fi daukan hankali su ne na ba da ‘yanci ga kananan hukumomi da kebe kujeru 111 wa mata don a zabe su a Majalisun Kasar, lamarin da ya sa Uwargidan Shugaban Kasa Aisha Buhari yin tattaki zuwa zauren Majalisar.
Uwargidan Shugaban Kasar Najeriya Aisha Buhari ta kai ziyarar ba-zata zuwa zaurukan Majalisar kasan guda biyu, wato da na Dattawa da ta Wakilai ziyara da ta ya zo daidai da lokacin da majalisar ke gabatar da gyara-gyaren kundin tsarin mulkin kasar, inda zuwan nata ya nuna alamar goyon baya ga aikin da Majalisar ta yi, musamman ma fannin da ya kebe wa mata kujera daya a kowace jiha tare da ta ‘Yan majalisar wakilai guda biyu, abinda ya sanya su dokin sanin cewa sun dade suna neman kari na mukaman siyasa da a yanzu kashi uku kachal suke da shi a majalisar dokokin kasar.
“Aisha Buhari ta ce ta zo ne ta saurari bayanai da aka yi a kan gyaran Kundin tsarin mulkin Kasa, musamman ma bangaren da aka ware domin mata. Ta ce ta ji dadi kwarai da wannan nasara da aka samu.
Farfesa Joy Ezeilo na cikin matan da suka dade suna fafutuka tun taron mata na Beijing da suka nemi a ba su kashi 35 cikin 100 na mukaman, ga bayanin da ta yi
Farfesa Joy Ezeilo ta ce “ Wannan babban ci gaba ne aka samu a gwagwarmayar da mata suke yi a Najeriya, domin mun dade muna fuskantar koma baya ta fannin siyasa tun daga 1999, idan aka ce muna da kashi 25 na mata a Majalisar kasa ai ci gaba ne sosai domin yanzu muna da kashi 13.5 cikin 100 na mata ne a Majalisar dokokin Najeriya.
Balaraba Muhammad ‘yar gwagwarmaya a birnin tarayya Abuja cewa ta yi ta ji dadin wannan nasara da aka samu.
A cewar dan majalisar dattawa Ahmad Babba Kaita wanda yana daya daga cikin wadanda su ka yi gyara kan kundin tsarin mulkin, babban abu mai muhimmanci a gyare-gyaren da aka yi shi ne a tabbata cewa abin da ‘yan Najeriya su ka zaba shi aka ba su, sai kuma ya kasance an yi zabe mai inganci wanda duk duniya za’a yarda da shi.”
An dade ana ce-ce-ku-ce da nuna dan yatsa a kan kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 da wasu ke kallon sojoji ne suka tsara shi kafin sake kafa mulkin dimokradiya, abin da ya sanya ya ke fuskantar gyare-gyare.
Saurari cikakken rahoton Medina Dauda daga Abuja: