Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dattawan Najeriya Ta Yi wa Kudurin Dokar Fansho Karatu Na Biyu


Majalisar Dattawan Najeriya (Facebook/Majalisar Dattawa)
Majalisar Dattawan Najeriya (Facebook/Majalisar Dattawa)

Majalisar Dattawa Najeriya ta yi wa kudurin dokar fansho karatu na biyu da zimmar kawo sauki wa tsoffin ma'aikata wajen samun hakkokinsu bayan sun kammala wa'adin aikin Gwamnati.

Wannan doka da aka yi wa lakabi da Dokar sake fasalin fansho Na shekara 2014 a karkashin gyaran kundin tsarin mulki na shekara 2022, an karanta ta ne a karon farko ranar 5 ga watan Nuwamba na shekara 2019.

A lokacin da ya jagorancin mahawara akan dokar a zauren majalisar dattawa, Sanata Aliyu Magatarkada Wammako, ya nemi a yi kwaskwarima ga dokar don samar da kaso mai ma'ana wanda ma'aikaci da ya yi ritaya zai iya samun hakkokinsa daga asusun ajiyarsa na ritaya.

Shi ma Sanata Istifanus Gyang wanda aka yi mahawarar tare da shi, ya bayyana ra'ayinsa a game da dokar inda ya ce sun yi muhawara kan kudurin dokar domin a kawo gyarar yadda kowane dan fasnho zai iya cin gajiyar kudaden na fansho da aka tara.

Sai dai wani dan fasnho Mahmud Jafaru, wanda tsohon ma'aikacin banki ne da ya yi ritaya, ya ce ba sa iya biyan bukatunsu nay au da kulluma kamar samarwa iyalansu abinci da biya kudaden makarantun yara.

Majalisa dattawa ta mika wannan kudurin dokar ga Kwamiti Mai Kula da harkokin Ma'aikata Gwamnati tareda wa'adin makonni hudu da a ka ba kwamitin ya kammala aiki, ya dawo wa majalisar da cikakken rahoto.

XS
SM
MD
LG