Wani ayarin masu gudanar da aiyukan jin kai a Kamaru ya kai ziyara gida gida a yankunan dake cikin kauyuka, domin bikin watan wayar da kai, kan cutar kansar mama, ko sankarar nono, inda suke ba mata shawara da su ziyarci asibitoci domin ayi musu gwaji kyauta.