Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ukraine Tayi Kira Ga Manyan Kasashen Yamma Dasu Takawa Koriya Ta Arewa Birki Kan Shirin Taimakama Rasha Yaki Da Ukraine.


Shugaban Ukraine Velodymyr Zelensky
Shugaban Ukraine Velodymyr Zelensky

Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya bukaci abokan huldar shi da su fa daina sa ido suna kallo, su hanzarta daukan matakan da suka dace na taka birki, kafin dakarun Koriya ta Arewa da aka aika Rasha su isa fagen daga.

Zelensky ya ankarar kan shirin da Ukraine keyi na kai hari kan sansanin da ake ba dakarun Koriya ta Arewan horo, yace, Kyiv na sane da inda wurin yake. To amma yace, Ukraine ba zata iya yin hakan ba, ba tare da samun umurni daga kawayen nata ba, nayin amfani da makaman zamani masu cin dogon zango, da za’a iya kai hari dasu har cikin kuryar Rasha.

Zelensky ya fada cikin wata wallafa ta kafar aikewa da sakonnin Telegram a ranar Juma’a cewa, a maimakon haka, sai ga shi Amurka ta sa ido tana kallo, Birtaniya na kallo, haka ma Jamus duk sun zuba ido suna kallo. Kowa na jiran yaga yadda dakarun kasar ta Koriya ta Arewa zasu yagalgala al’ummar Ukraine.

A ranar Alhamis gwamnatin Biden tace, yanzu haka wasu dakarun koriya ta arewa su 8,000 na hallare a yankin Kursk na Rasha dake kusa da kan iyaka da Ukraine, inda suke shirye shiryen taimakama Kremlin fada da dakarun Ukraine a nan da yan kwanaki masu zuwa.

A ranar Asabar, sojojin leken asirin Ukraine, suka ce, an kai yan Koriya ta Arewa su sama da 7,000 shirye da kayayyakin yaki da makaman Rasha zuwa yankunan dake kusa da Ukraine. Wata hukumar kasar da aka sani da GUR, tace ana ba dakarun Koriya ta Arewan horo a wurare 5 dake can gabashin Rasha, ba tare da bayyana majiyar labarin ba.

Shugabannin yammaci sun bayyana kai dakarun kasar ta Koriya zuwa Rasha, a matsayin wani yunkurin fadada yakin, da ka iya dagula hulda a yankin Indo-Pacific, da kuma bude kofar shigar da fasaha daga Moscow zuwa Pyongyang da ka iya fadada barazanar makaman nukiliyar kasar Koriya ta arewa.

A ranar Juma’a ministan harkokin wajen Koriya ta Arewa Choe Son Hui ta gana da takwaran ta na Rasha a Moscow.

Shugabannin Ukraine sun sha nanata fadin cewa, suna bukatar izni domin yin amfani da makaman kasashen yamma wajen kai hari kan wuraren ajiye makamai, filayen jiragen sama da sansanonin soji dake nesa daga kan iyaka, da zai sa Rasha ta ji a jika ta nemi a zauna lafiya., Jami’an ma’aikatar tsaron Amurka sun maida martani inda suka bukaci takaita makamai masu linzami, da cewa ai tuni Ukraine ke amfani da jirage marasa matuki masu cin dogon zango wajen kai hari cikin Rasha.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG