Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Isra’ila Tace Ta Kammala Kai Hare Haren Data Tsara Kaiwa Iran


Shugaban Isra'ila Benjamin Netanyahu
Shugaban Isra'ila Benjamin Netanyahu

Isra’ila tace, ta kammala wani gagarumin hari akan Iran bayan sama da shekara guda da aka kwashe ana bata kashi, daya samo asali da wani hari da mayakan Hamas da Iran ke marawa baya suka kai kan kasar Isra’ila, daya rikide zuwa wani rikicin da kai tsaye ya damalmale Iran da yan koren ta a yankin.

Cikin wata sanarwa da aka fitar da safiyar Asabar, Rundunar dakarun tsaron Isra’ila tace, jiragen yakin ta sun koma gida lami lafiya, bayan kai wani tsararren harin soji a wurare da dama a Iran. Ta fitar da sanarwar ne kimanin sa’oi 4 bayan samun rahoton farko daya bulla na wata fashewa a Iran da kimanin karfe 2:30 na asuba a birnin Tehran.

Rundunar dakarun tsaron Isra’ilan ta kara da cewa, bisa rahotannin sirrin data samu, dakarun saman ta, sun kai hari kan masana’antar Kera makamai masu linzami da ake amfani da ita wajen kera makamai masu linzamin da Iran ta rika harbawa cikin Izra’ila a shekara gudan data wuce. Rundunar tace, wadannan makamai masu linzami nayin barazana kai tsaye ga al’ummar Isra’ila.

Haka zalika, rundunar dakarun tsaron ta kai wani hari ta sama da ta kasa kan wasu muhimman wurare a Iran, da nufin karya laggon irin hare haren da Iran din ke kaiwa Isra’ila.

Mai Magana da yawun rundunar, Rear Admiral Daniel Hagari ya shaidawa manema labarai cewa, Isra’ila tayi nasara a hare haren ta sama data gudanar, duk da dai anan take bata gabatar da wata sheda akan ikirarin nata ba.

Shafin kafar labarum Iran IRNA ta jiyo hukumar tsaron sararin saman kasar na cewa, Isra’ila ta kai hari kan cibiyoyin soji a birnin Tehran da yankin arewacin Khuzestan da Ilam. Ta kara da cewa, dakarun na Iran sunyi nasarar dakile da dama daga hare haren, su ka tabbatar da cewa, barnar da harin ya haifar ba ta da yawa.

Mataimakin shugaban Iran na farko Mohammad Reza Aref ne kadai babban jami’i da ya tofa albarkacin bakin shi akan hare haren na Isra’ila na safiyar Asabar. Ya wallafar tutar kasar musuluncin a shafin sadarwar zamani na X inda ya rubuta cewa’ Shugabannin Iran sun tozarta makiya kasar mu ta haihuwa.’

Hukumomin na Iran basu gabatar da wata shedar da ta nuna cewa sun dakile hare haren da Isra’ilan ta kai mata ta sama ba, ko cewa ba wata barna da ta abku. To sai dai kafar yada labarum kasar ta sanar da jiyo dakarun Iran na cewa, harin na Isra’ila ya hallaka sojoji biyu.

Wani babban jami’in Amurka ya shaidawa manema labarai cewa, Isra’ila ta kai tsararrun hare hare ta sama kan wuraren soji dabam dabam a sassan Iran da wajen wuraren dake da yawan mutane.

Dandalin Mu Tattauna

TASKAR VOA: Yadda Tsofaffi Ke Fama Da Lalular Yanar Ido A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:26 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG