Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Trump Na Ci Gaba Da Bayyana Sunayen Ministocin Gwamnatinsa


Zababben Shugaban Amurka mai jiran gado Donald Trump.
Zababben Shugaban Amurka mai jiran gado Donald Trump.

Zababben shugaban Amurka Donald Trump na aza kaimi wajen saurin hada hancin gwamnatin shi, da jiga-jigan ‘yan jam’iyyar Republican, wadanda da mafi yawansu suka kasance masu biyayya gare shi a shekaru hudun da ya kasance baya ofis.

Kamar yadda majiyoyin yada labarai na Amurka daban-daban ke ruwaitowa, akwai alamun nada Sanatan jihar Florida Marco Rubio, a matsayin sakataren harkokin waje, mukamin diplomasiyya mafi girma a kasar, sai kuma gwamnar jihar South Dakota, Kristi Noem, a matsayin sakatariyar tsaron ma’aikatar cikin gida.

A watannin baya, daga Rubio har Noem sun kasance a jerin sunayen wadanda aka yi zaton dayan su zai kasance a matsayin mataimakin shugaban kasa ga Trump.

Yayin da daga bisani Trump ya zabi Sanatan jihar Ohio JD Vance, wato mataimakin shugaban kasa mai jiran gado, ya hau tikin takarar shi a karkashin jam’iyar Republican, Rubio da Kristi sun ci gaba da kasancewa na hannun daman shi, har ya kai ga nasara a zaben da aka gudanar da ya samu nasara kan yar jam’iyar Democrat, mataimakiyar shugaban kasa Kamala Harris.

Trump ya kuma sanar da cewa hamshakin attajirin nan mai suna Elon Musk, da kuma dan kasuwa kuma tsohon dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Republican Vivek Ramaswamy, zasu jagoranci abin da ya kira ma'aikatar harkokin gwamnati.

Sanarwar ta ce za su ba da shawarwari da jagoranci don “samar da manyan garambawul” na gwamnatin tarayya.

Trump ya kuma sanar a ranar Talata cewa, ya zabi William McGinley a matsayin lauya kuma mai ba da shawara a fadar White House.

Trump ya kuma amince da Michael Waltz, dan Majalisar Dokokin jihar Florida, a matsayin mai ba shi shawara kan harkokin tsaro. Waltz a farkon wannan shekarar ya goyi bayan yunkurin ‘yan Majalisar Dokokin Republican da aka dade na yi na sake sunan tashar jirgin saman Washington da a saka sunan Trump.

Dandalin Mu Tattauna

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG