Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Ja Hankalin Kasashen Turai Da Kada Su Maimaita Kuskuren Sa Shinge Tsakanin Su Da Zababben Shugaban Amurka Donald Trump


Zababben shugaban Amurka Donald Trump
Zababben shugaban Amurka Donald Trump

A ranar Asabar ministan tsaron Lithuana yace, kada kasashen tarayyar turai su sake yin kuskuren haifar da shinge tsakanin su da zababben shugaban Amurka Donald Trump, maimakon haka kamata yayi su hada kai kan al’amurran da zasu amfane su baki daya.

A ranar Asabar ministan tsaron Lithuana yace, kada kasashen tarayyar turai su sake yin kuskuren haifar da shinge tsakanin su da zababben shugaban Amurka Donald Trump, maimakon haka kamata yayi su hada kai kan al’amurran da zasu amfane su baki daya.

Ko da kuwa, Trump zai sake yin aiki da abinda Laurynas Kasciumas ya kira gwangila a huldar su da shi. Kasciunas ya zayyna wuraren da Turai zata iya hada guiwa da sabon shugaban kasar, kamar inganta zuba jari a bangaren tsaro, da yadda kasashen Turai zasu rika amfani da makaman Amurka da hada kai wajen takawa China da Iran birki.

Kasciunas ya shaidawa kafar labaran Associated Press cewa, inda suka yi dan kuskure a baya, lokacin da aka zabe shi bayan yayi nasara akan Hillary Clinton, abu ne da ko kusa ba za’a amince da shi ba, lokacin aka dora shamaki akan batun rashin da’a.

Kasciunas yace yana tunanin hakan ba dai dai bane. Yana Magana ne a gefen taron kwanaki uku a Prague, da ya maida hankali akan karfin sojin tarayyar Turai da kasashen tsallaken kogin atlantika.

A farkon wa’adin shi a shekarar 2017-2021, Trump ya tilastawa manbobin tarayyar Turai dake kungiyar kawancen tsaro ta NATO, kashe karin kudi a bangaren tsaro, har sama da kashi 2% na abinda kasashen ke samarwa a cikin gida, da kuma rage dogaron su akan agaji daga sojin Amurka.

Wannan shine abunda kawayen kasashen suka rika yi. Adadin manbobi 23 ne ake sa ran zasu kai ga hasashen kashi 2% a bana, idan aka kwatanta da adadin shekaru 3 zuwa 10 da suka wuce. NATO tace, tuni kasar Lithuania ta zarce kashi 2 da rabi daga cikin 100, a hankoron da take na kaiwa kashi 4% da zai zarta na Amurka.

Cibiyoyin tsaron Turai sun tabuka wajen kara azama kan wasu abubuwan bayan cikakkiyar mamayar da Rasha ta yiwa Ukraine a shekarar 2022, duk da dai kasashen Turai su ma sun bada gudummuwar makaman su ga Ukraine, su ka kuma cigaba da dogaro akan Amurka, a matsayin wani muhimmin bangare ga karfin sojin su, kamar yadda yazo a rahoton da cibiyar kasa da kasa ta nazarin manyan al’amurra mai mazauni a London ta wallafa, ta sanar a yayin taron na Prague.

Lithuania wadda ke makwabtaka da yankin Kalimingrad na Rasha ta bangaren yamma, da kuma Belarus ta bangaren gabashi, ta cigaba da kasancewa jagaba wajen sayen makamai daga Amurka, a tsakanin kasashen Baltic 3.

Ministan, wanda kasar shi ke kan yar tsama da China game da batun Taiwan, shima yayi magana yana mara baya ga takunkumin da tarayyar Turai ta kakabama Iran.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG