Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hare-Haren Da Muka Kai Kan Iran Sun Cimma Manufa - Isra'ila


Shugaban Isra'ila Benjamin Netanyahu
Shugaban Isra'ila Benjamin Netanyahu

Kakakin rundunar tsaron Isra'ila Daniel Hagari ya bayyana a wani taron manema labarai da aka watsa ta gidan talabijin cewa, “bisa umarnin tsarin siyasa, sun kai hare-hare kan wurare daban-daban a Iran.”

Ya kara da cewa “ciki har da kai hari kan ma’aikatar kera makamai masu linzami da Iran ke amfani da su wajen kai wa Isra’ila hari sama da shekarar da ta gabata. Hakazalika sun kai hari kan makaman kakkabo makamai masu linzami ta sama, don bai wa Isra’ila damar kai hare-harenta.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya ruwaito cewa, shafin sadarwa na yanar gizo na ma’aikatar tsaron kasar Iran IRNA na cewa, kasar Isra’ila ta kai hari kan cibiyoyin soji a Tehran da kuma yammacin lardunan Khuzestan da Ilam.

Ya ce sojojin Iran “cikin nasara” sun katse mafi yawa daga cikin hare-haren, tare da tabbatar da cewa ba su yi barna mai yawa ba.

A ranar Lahadi, Shugaban Addini a Iran, Ayatollah Ali Khamenei ya ce, ba ya goyon bayan yin ramuwar gayya, maimakon hakan ya ce a yi takatsantsan, kar a zafafa kar kuma a yi watsi da lamarin.

Khamenei wanda ke da ta cewar karshe akan lamurra, ya kara da cewa, ya rage na hukumomin su san yadda za su yi amfani da karfinsu wajen isar da muradun Iraniyawa ga gwamnatin Isra’ila da daukar matakan da za su yi wa kasar daidai.

A ranar Litinin kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya zai zauna, biyo bayan rokon da Iran din ta yi bayan harin da ta kai wa Isra’ila, dayin ikirarin cewa, Isra’ilar ta keta haddin dokokin kasa da kasa.

Wani mai sharhi a Isra’ila ya ce, kudurin takaita hare-haren ga wuraren soji kawai y a ba Iran damar ja da baya daga tunanin fadada yakin da Isra’ila.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG