A ranar Litinin Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres, ya yi kira da a hanzarta kawo karshen yakin basasar da aka shafe watanni 18 ana yi a Sudan.
Yakin na Sudan ya shafi miliyoyin mutane ta fuskar raba su da muhallansu, haddasa karancin abinci da salwantar da rayukan jama'a da dama.
Guterres ya ce, wahala karuwa take a kullum rana ta Allah, a yayin da yake nuna matukar damuwa game da halin da ake ciki a yankin El Fasher na arewacin Dafur, inda yaki ya ci gaba da rincabewa tun a a tsakiyar watan Afrilu.
“Na firgita matuka da ci gaba da hare-haren da rundunar dakarun kar ta kwana ta RSF ke kai wa kan farar hula a El Fasher da yankunan da ke kewaye, da ya hada har da wuraren mutanen da aka daidaita.” In ji Guterres.
Jakadar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Linda Thomas- Greenfield, ta bukaci mambobin majalisar da su yi amfani da duk wata dama da suke da ita wajen magance matsalar.
Dandalin Mu Tattauna