Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Donald Trump Da Kamala Harris Na Bukatar Kara Zage Damze Domin Samun Nasara A Jihar Georgia A Zaben 2024


Tsohon shugaban Amurka Donald Trump da mataimakiyar shugabannkasa Kamala Harris
Tsohon shugaban Amurka Donald Trump da mataimakiyar shugabannkasa Kamala Harris

Jihar Georgia ta rika nuna alamun sake zaben tsohon shugaban Amurka Donald Trump a farko farkon yakin neman zaben shugabancin Amurka a shekarar 2024, lokacin da shugaba Joe Biden ke bisa takarar, to amma mataimakiyar shugaban kasa Kamala Harris ta maida wasa sabo zuwa ga jam’iyar Democrat.

A yanzu dai ana daukar Georgia a matsayin daya daga cikin manyan jihohin raba gaddama a sakamakon zaben, wanda duk da haka ake ganin Harris nada saura zage damtse.

Duk da dai cewa, Biden ya lashe Georgia a zaben shekarar 2020, da ya kai ga karshen nasarar da jam’iyar Republican ta saba yi a jihar tsawon shekaru 30, yayi nasarar ne da dan kankanin rinjayen kuri’u.

Idan har zatayi nasara, to wajibi ne Harris ta samu gagrumar nasarar kuri’un bakar fatar wadanda bisa al’ada suka saba zaben jam’iyar Democrat. To amma shima Trump ya rika zawarcin wadannan masu kada kuri’ar, da sakamakon ra’ayoyin jama’a da aka rika tattarawa ya nuna ya rika samu nasara akai.

A zaben da zai kasance na kud da kud, al’amurra da dama na iya tasiri a sikelin kowane daga cikin yan takarar, da ya hada da fannin tattalin arziki, shigi da fici, yancin zubar da ciki da dokar mallakar bindiga, da uwa uba, tabbatar da dorewar Democradiyya.

Jihar Georgia wuri ne dake kan takaddama inda ake zargin Trump da makarraban shi da hadin bakin neman sauya kayen da ya sha a zaben shekarar 2020.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG