Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Aika Boyayyun Sakonnin Batunci Da Tsokana Ga Amurkawa Bakar Fata A Wasu Jihohin Amurka


Tutar Amurka
Tutar Amurka

Hukumomin tarayya da na jiha na binciken wani sakon wasika na nuna wariyar launin fata da aka rika turawa a boye ga Amurkawa bakar fata a sassan kasar.

Hukumomin tarayya da na jiha na binciken wani sakon wasika na nuna wariyar launin fata da aka rika turawa a boye ga Amurkawa bakar fata a sassan kasar cikin makon nan, inda aka rika shaida musu cewa kamata yayi a bautar da su, lamarin da yanjanyo gagarumin yin Allawadai da kuma gargadi.

Kungiyar kare hakkin bil’adama ta NAACP tace, sakonnin sun bukaci, wadanda aka turawa a jihohi da dama, da suka hada da jihohin Alabama, North Carolina, Pennsylvania da jihar Virginia, da su kai kan su gonaki domin tsinkar auduga, wata bakar kalma dake inkiya ga lokuttan baya, da aka rika bautar da bakar fata a Amurka.

Har yanzu dai ba’a san wadanne mutane ko kungiyoyi bane ke bayan irin wadannan sakonnin da ake aikewa, da kuma adadin wadanda suka samu sakonnin.

Mutane a jihohi akalla 21 sun samu sakonnin, da ya hada har da makarantun sakandire da kwalejoji, kamar yadda kafar CNN da Associated Press suka ruwaito.

Shugaban kungiyar kare hakkin ta NAACP mai yada manufofin tabbatar da adalci ga hakkokin Amurkawa bakar fata, Derrick Johson ya fada cikin wata sanarwa cewa, ko kusa lamarin baiyi daidai ba, kuma ba za’a yarda a bar hakan ya samu wurin zama ba.

Yace, wadannan sakonnin alama ce mai firgitarwa game da takale takale da manufofin kungiyoyin masu nuna kyama ga banbancin launin fata a sassan kasar.

Da dama daga cikin al’ummomin Amurkawa bakar fata sun ce dama sun san za’a rina, tun bayan da Donald Trump na jam’iyar Republican wanda ya lashe zaben shugaban kasar na ranar Talata, yayi nasara kan Kamala Harris ta jam’iyar Democrat, a wanda zai shiga office a ranar 20 ga watan janairu idan Allah ya kai mu.

Cikin wata sanarwa a ranar Juma’a, mai magana da yawun shi, Karoline Leavit tace, ko da wasa, ba abun da ya hada yakin neman zaben Trump da wadannan sakonnin wasikar.

Wani mai Magana da yawun fadar white House ta Biden, Robyn Patterson ya fada cikin wata sanarwa a jiya Juma’a, a yayin da yake tabbatar da gudanar da binciken, ya bayyana yin allahwadai da kakkausan lafazi da wadannan sakonnin kin jinni, da duk wani mai harin Amurkawa kan launi ko asalin su.

Yace nuna kyamar launin fata bas hi da mazauni a Amurka. Hukumar sadarwa ta kasa ta fada a ranar Juma’a cewa, hukumar na daga cikin masu bin diddikin lamarin.

TexNow tace, akwai wani mutum guda ko mutane 2 da suka aika sakonnin batunci ta kafar ta, kuma a cikin sa’a daya aka rufe su, ya kara da cewa, an aike da sakonnin wasikar ne ga cibiyoyin aikewa da sakonni dabam dabam a fadin kasar, a wani abun da ta kira’’ kai hari’ inda ya sha alwashin yin aiki da jami’an tsaro.

Suma hukumomin kananan hukumomi na gudanar da bincike akan lamarin, inda wasu manyan masu shari’a na jihohi suka bukaci wadanda aka aikewa sakonnin dasu kai rahoto ga bangarorin kare hakkin bil’adama dake yankunan su.

Wasu makarantun gunduma sun yi gargadi tare da bukatar dalibai da iyayen su, da su kai rahoton samun irin wadannan sakonni ga malaman makaranta da hukumomi.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG