Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masu Zanga Zanga A Isra’ila Sun Zargi Praiminista Netanyahu Da Kin Kawo Karshen Yakin Da Kasar Keyi A Gaza


Shugaban Isra'ila Benjamin Netanyahu
Shugaban Isra'ila Benjamin Netanyahu

A ranar Asabar daruruwan mazu zanga zanga a birnin Tel Aviv na kasar Isra’ila suka amayar da takaicin su kan gazawar gwamnati na cimma yarjejeniyar da zata maido sauran wadanda ake garkuwa dasu a Gaza zuwa gida.

Masu zanga zangar da suka rika daga tuta a yankin kasuwancin kasar, sun rika daga kwalaye dake dauke da rubutu dake cewa, ‘yarjejeniya a yanzu,’ ‘a dakatar da yakin,’ ‘ba zamu yi watsi da su ba,’ Masu zanga zangar sun rika buga ganguna suna ihu da fadin cewa, ‘me yasa har yanzu suke cikin Gaza?’’

Wani daga cikin masu zanga zangar, Zahiro Shahar mai shekaru 52 a duniya, ma’aikacin banki dake zaune a birnin Tel Aviv, yace an samu damarmaki bila adadin na kawo karshen rikicin, amma gwamnati tayi patali da su, daya bayan daya.

Shima wani mai fafutukar ganin an sako sauran wadanda ake garkuwa dasu, da ya fito zanga zangar, mai suna Mor, wanda aka kashe kawun sa mai suna Avraham Munder a lokacin da ake tsare da shi a Gaza, yace tashin hankalin karuwa kawai yake yi, mako bayan mako, ba tare da ganin karshen shi ba.

Masu caccaka sun rika tambayar dalilin da yasa har yanzu aka gaza cimma yarjejeniyar kawo karshen yakin, musamman ganin cewa, a yanzu Isra’ila ta cimma da yawa daga cikin gurin ta a yakin, da ya hada da kisan shugaban Hamas Yahya Sinwar a watan jiya.

Jami’an Isra’ila da na Amurka da wasu masu sharhi sunce, Sinwar shine ya kasance cikas ga cimma yarjejeniyar sulhu tsakanin Isra’ila da Hamas.

Wata yar zanga zangar mai kin jinin gwamnati, Ifat Kalderon, wadda ta bayyana tsoran ta game da makomar dan’uwanta da har yanzu ke tsare a Gaza, ta dora laifin kan Benjamin Netanyahu, priministan Isra’ila mafi dadewa a kan karaga.

Ifat Kalderon mai shekaru 50 da haihuwa. tace, duk wata yarjejeniyar da aka fara, sai yayi mata kafar angulu. A ko yaushe yakan dora laifin hakan akan Sinwar, kuma a yanzu Sinwar ya bar duniya. Amma a ko yaushe sai ya kirkiro wani dalili.

Ta kara da cewa,’ yaki ne da ake zubar da jinni a cikin shi, abun ya isa haka. Sojoji da dama sai mutuwa suke yi, da ma sauran mutanen gari a duk bangarorin biyu, da basu ji ba basu gani ba’.

Wasu mahalarta zanga zangar, da iyalan wadanda yan’uwan su ke tsare suka shirya, sun kuma yi kira kan halin da dakarun kasar ke ciki, da suka ce an gajiyar da su a yakin da Isra’ilan keyi da Hamas a Gaza.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG