Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Dakarun Saudi Arebiya Biyu A Yayin Wani Hari A Yemen


Muhammad Bin Salman na Saudi Arebiya
Muhammad Bin Salman na Saudi Arebiya

A ranar Asabar, kafar yada labaran Saudiyya tace, an kashe jami’an sojin kasar biyu a yayin wani hari a Yemen, akace, wanda ya kai harin na da alaka da ma’aikatar tsaron Yemen.

A ranar Asabar, kafar yada labaran Saudiyya tace, an kashe jami’an sojin kasar biyu a yayin wani hari a Yemen, inda akace, wanda ya kai harin na da alaka da ma’aikatar tsaron Yemen.

Dakaru biyu sun yi shahada, wani guda kuma ya sami rauni sakamakon harin ragoncin da aka kai a ranar Juma’a cikin sansanin sojin dake birnin Seiyun, cewar kafar yada labarun Saudi Arebiya, kamar yadda ta jiyo da ga mai magana da yawun ma’aikatar tsaron Birgediya janar Turki al-Maliki.

Saudi Arebiya ta yo gangamin wani hadin guiwa daga kasashen duniya domin shiga tsakani a Yemen a tallafawa gwamnatin da duniya ta amince da ita, a shekarar 2015, bayan da mayakan Houthi masu samun goyon bayan Iran sun kwace babban birnin kasar Sanaa, shekara guda kafin nan.

Seiyun ya kasance a gwamnatin Hadhramout, wadda ta fadi a karkashin ikon gwamnatin da duniya ta amince da ita a Yemen.

Dakarun hadin guiwan da aka girke a sansanin da aka kaiwa harin, na tallafawa ne wajen bayar da horo ga dakarun cikin gida domin su yaki ta’addanci da fasakwabri, cewar kafar labarum Saudi Arebiya.

Kafar ta kara da cewa, ankai harin ne a yayin da ake tsaka da bayar da horon motsa jiki, ba tare da cikakken karin haske kan yadda lamarin ya abku ba, da wanda ya kai harin, ko matsyin shi.

Wani jami’in Yemen ya shaidawa kafar labarum AFP cewa, lamarin ya samo asali ne daga cacar baki tsakanin bayamanen da ya kitsa harin da yan Saudiyya, wanda daga bisani lamarin ya kai ga musayar wuta.

Kafar labarun Saudiyan tace, wanda ya yi aika aikar baya wakiltar jami’an ma’aikatar tsaron Yemen, wanda ke girmamawa tare da sanin muhimmancin rawar da dakarun hadin guiwar ke takawa wajen marawa gwamnati baya.

Kafar labaran tace, an kai gawawwakin dakarun biyu, da wanda ya ji raunin zuwa Saudi Arebiya.

Rahoton ya cigaba da cewa, dakarun hadin guiwar zasu yi aiki tare da ma’aikatar tsaron Yemen domin bin diddigi kan hanyoyin gudanar da bincike domin gano dalili da manufar kai harin, da kama wanda ya kitsa harin domin ya fuskanci hukunci.

Majalisar Dinkin Duniya tace, yakin na Yemen ya kashe dubban daruruwan mutane, ko dai a fada ko kuma daga masifun da fadan ya janyo irin su rashin abinci.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG