Jami'in ayyukan jinkai na majalisar dinkin duniyar ya ce "koda baya ga matsalar yunwar, an kiyasta kimanin yara dubu dari bakwai ka iya fuskantar matsanancin karancin abinci mai gina jiki da ka iya yi wa rayuwarsu barazana.''
Biyo bayan nadin sabbin manyan hafsoshin tsaron da sabon Shugaban Najeriya Bola Ahmad Tinubu Yayi, a ranar Litinin, wakilin Muryar Amurka Hassan Maina Kaina Ya duba Tarihin wadannan manyan shugabannin rundunonin sojojin kasar.
Zargin da tsohon jagoran masu tada kayar baya a yankin Niger Delta Asari Dokubo ya yi wa rundunar sojin Najeriya na cewa suna taka rawa wajen satar mai, na ci gaba da jan hankali.
Watanni shida bayan zarginta da hallaka gwamman makiyaya, rundunar sojojin saman Najeriya ta bada bahasi cewa ‘yan ta'adda ta halaka a wannan farmaki.
Kafin dai su tafi da basaraken, ‘yan bindigar sun kuma abka wani gidan makwabci da ke kusa inda shi ma suka sace shi a daidai lokacin da suke ta harba bindiga.
Kungiyoyin kwadago a Najeriya sun ja daga inda suka ce lallai janye tallafin man fetur da gwamnatin Tinubu ta yi ba za ta lamunta da shi ba.
A cewar Janar Monguno shugaba Tinubu ya ce dole ne hukumomin tsaron kasar suyi aiki tare bisa tsari sannan ake tuntuba.
Tun da farko hukumar yaki da cin hanci da rashawa wato EFCC, ta bayyana cewa ta kadu matuka da yadda jami'an hukumar DSS suka mamaye mata ofis da ke birnin Lagos inda suka tare kofar shiga hukumar da motoci masu sulke.
A wani mataki na karfafa gwiwar dakarun Najeriya da ke fafatukar kare kasar, an karrama sojojin kasar da su ka kwanta dama yayin aiki ma kasar.
Najeriya na jagorantar cimma wani muradi na kungiyar tarayyar Afirka na samar da wata rundunar sojojin ruwa ta kasa-da-kasa makamanciyar ta yankin tafkin Chadi don aikin samar da tsaro a yankin gabar tekun Guinea.
Hedikwatar rundunar mayakan ruwan Najeriya ta gano masu ma ta sojin gona a matsayin sojojin ruwa
Rundunar sojin ruwan Najeriya za ta kulla yarjejeniyar aiki da wasu kasashen Afirka don kara tunkarar yanayin tsaro a Gabar Tekun Guinea.
Rundunar 'yan sandan yankin babban birnin Tarayyar Najeriya ta ce jami'anta sun kai wani samame a cikin dajin Udulu da ke karamar hukumar Gegu a jihar kogi da ke makwabtaka da dajin Sardauna na jihar Nassarawa da dukkanninsu ke makwabtaka da yankin babban birnin Tarayyar.
Sa dai tambayar da ake yi ita ce, shin tsaron ya samu? wadanda ke yankunan da kalubalen tsaron ke addaba sun yi tsokaci a shirin Tubalin na Tubalin Tsaro.
Rundunar 'yan sandan Najeriya ta ce ta sami nasarar cafke kwamishinan hukumar zaben ta kasa INEC na Jihar Adamawa, Hudu Ari, wanda ya yi riga-malam masallaci wajen ayyana sakamakon zaben gwamnan jihar Adamawa tun ba'a kammala tattara sakamakon baki daya ba.
Rundunar Sojin dai ta gudanar da ayyukan raya ilimin ne domin kara kulla alaka da fararen hula.
Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, gwamnatinta ta samu nasara ainun wajen shawo kan matsalolin tsaro da ake fuskanta a Najeriya.
Rikicin kabilanci ya da ya barke a unguwar Gwarinpa da ke tsakiyar birnin Abuja tsakanin Hausawa da Gwarawa ya yi sandin mutuwar mutum daya.
Yayin da sauran kasashen duniya suka yi nisa da kwashe 'yan kasashensu daga Sudan mai fama da tashin hankali, Najeriya ta ce yau ko gobe za ta fara jigiliar 'yan Najeriya mazauna Sudan wadanda suka fara kokawa da irin tsaka mai wuyar da suke ciki.
Domin Kari