Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sabbin Manyan Hafsoshin Tsaron Najeriya


Najeriya sojojin a rantsar, Abuja, Mayu 29, 2015.
Najeriya sojojin a rantsar, Abuja, Mayu 29, 2015.

Biyo bayan nadin sabbin manyan hafsoshin tsaron da sabon Shugaban Najeriya Bola Ahmad Tinubu Yayi, a ranar Litinin, wakilin Muryar Amurka Hassan Maina Kaina Ya duba Tarihin wadannan manyan shugabannin rundunonin sojojin kasar.

Manjo Janar Christopher Gwabir Musa, sabon babban hafsan hafsoshin sojan Najeriya dan asalin yankin karamar hukumar Zangon Kataf ne a jihar Kaduna. An haife shi a shekarar 1967 a birnin Sakkwato.

Dan kwas na 38, ya kammala makarantar horas da hafsoshin soja ta NDA a shekarar 1991.

Musa ya halarci kwasa-kwasai da dama a ciki da wajen Najeriya irin su China da Amurka. Ya rike mukamai da dama a gidan soji, ya kuma yi aiki a karkashin rundunar majalisar dinkin duniya.

Janar Musa ya sami lambobin girmamawa daban-daban har sama da 23, ya kuma taka rawa sosai a matsayin kwamandan rundunar yaki da Boko Haram.

Kafin dai nadin nasa, shine kwamandan rundunar soji masu yaki na gaba-da-gaba, wato infantery na Najeriya.

Manjo Janar Taoreq Abiodun Lagbaja, shine sabon babban hafsan hafsoshin sojojin kasa wanda zai canji Laftanar janar Farouq Yahaya. Kuma an haife shi ne a karamar hukumar Illokun-Irepodu da ke jihar Osun a shekarar 1968.

Janar Lagbaja, ya kammala makarantar hafsoshin soji ta NDA a shekara ta 1992. Ya kuma hallarci kwalejin horas da dabarun yaki ta Amurka bayan kwasa-kwasai da dama da yayi a cikin gida Najeriya da ma Afirka. Haka kuma ya kuma sami horon yaki a sama, akan tudu da kuma a cikin ruwa.

Ya rike mukamai da dama a gidan soji. Na baya-bayan nan da ya rike shine babban kwamandan runduna ta daya na sojin Najeriya mai shelkwata a Kaduna, inda ya taka rawa sossai wajen yaki da ‘yan bindiga.

A ta bakin tsohon kwamisahan tsaro na jihar Kaduna Samuel Aruwan, "Lagbaja gwarzo ne wanda bai da tsoro. Soja ne wanda shi da kan shi yake jagoranci a filin daga."

Air Vice Marshal Hassan Bala Abubakar, shi ne sabon babban hafsan sojin saman Najeriya.

Dan asalin yankin karamar hukumar Shanono a jihar Kano, an haife shi a shekatar 1970 kuma ya kammala makarantar horas da sojin Najeriya wato NDA a shekarar 1992.

AVM Abubakar, wanda matukin jirgin sama ne, ya halarci makarantar horas da dabarun yaki ta kasar Masar, ya kuma taba rike kwamandan matuka jirgin saman na fadar shugaban kasa.

Kafin a yi masa wannan mukami shi ne babban hafsa mai kula da inganci da aikace-aikace a shelkwatar sojin saman Najeriya.

Rear Admiral Emmanuel Ogala shi ne sabon babban hafsan sojan ruwan Najeriya. Ogala dan asalin dan jihar Enugu matukin jirgin ruwan yaki ne, dan kwas na 39, ya kuma rike mukamai dabam dabam kafin nadin nasa.

A saurari cikaken rahoton Hassan Maina Kaina:

Tarihin Sabbin Manyan Hafsoshin Tsaron Najeriya.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:05 0:00
XS
SM
MD
LG