Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Cafke Wani Mai Safarar Miyagun Makamai Kan Titin Abuja-Nassarawa

Abubakar Muhammad aka Abu Direba - Mai safarar miyagun makamai
Abubakar Muhammad aka Abu Direba - Mai safarar miyagun makamai

Hadakar jami'an tsaron Najeriya da suka hada da na farin kaya - DSS, sojoji da ‘yan sanda sun sami nasarar cafke wani kasurgumin mai safarar miyagun makamai, a yayin wani sintirin gwiwa a jihohin Kogi da Nassarawa, musamman akan babbar hanyar Abuja zuwa Keffi .

ABUJA, NIGERIA - Wata sanarwa da kakakin hukumar DSS na kasa DR. Peter Afunyaya ya aikewa sashin Hausa na Muryar Amurka na cewa jami'an tsaron sun cafke Abubakar Muhammad da ake kira Abubakar Direba, da makamai da harsasai manya har guda dari hudu da tamanin da shida, abubuwan fashewa ashirin da hudu, da kudade a cikin wata mota kirar Gulf.

Bindigogin da aka samu lokacin kama Abubakar Muhammad aka Abu Direba - mai safarar miyagun makamai
Bindigogin da aka samu lokacin kama Abubakar Muhammad aka Abu Direba - mai safarar miyagun makamai

Bugu da kari, cikin aikin na hadin gwiwa, jami'an tsaron sun kuma kai wani samame a maboyar jagoran ‘yan ta'addan nan na jihar Kogi mai suna Kabir Bala da ake yiwa lakabi da Okwo.

Dan ta'addan da sauran mutanensa sun budewa jami'an tsaron wuta inda nan take su ma suka maida martani har daga karshe suka bindigeshi.

Harsasai da aka cafke daga wurin buyar Abubakar Direba mai safarar miyagun makamai
Harsasai da aka cafke daga wurin buyar Abubakar Direba mai safarar miyagun makamai
Bindiga da aka samu lokacin kama Kabir Bala aka Okwo - Jagoran ‘yan ta’addan Jihar Kogi
Bindiga da aka samu lokacin kama Kabir Bala aka Okwo - Jagoran ‘yan ta’addan Jihar Kogi

An sami babbar bindiga kirar Ak 47, da wasu bindigogi na gargajiya guda shida, wayoyin salula da layu da wasu sauran abubuwa.

Layu da wasu tarkace da aka samu lokacin kama Kabir Bala aka Okwo - Jagoran ‘yan ta’addan Jihar Kogi
Layu da wasu tarkace da aka samu lokacin kama Kabir Bala aka Okwo - Jagoran ‘yan ta’addan Jihar Kogi

Hukumar tsaro ta DSS ta nemi jama'a musamman masu mu'amala da wuraren hada-hadar jama'a kamar kasuwanni da shaguna da su rika yin kaffa-kaffa da takatsantsan, sannan su sa ido kuma su kai rahoton duk wani motsi da basu yarda da shi ba ga jami'an tsaro.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG