Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Karon Farko Shugaba Tinubu Ya Gana Da Sabbin Manyan Hafsoshin Najeriya


Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu

Shugaban Najeriya Bola Tinubu a karon farko ya yi ganawar keke da keke da sabbin manyan hafsoshin kasar bayan nadinsu makonni biyu da suka shige.

ABUJA, NIGERIA - Mai baiwa shugaban kasa shawara a kan tsaron kasa, Mallam Nuhu Ribadu ne ya jagoranci manyan hafsoshin da Sufeta Janar na ‘yan sanda a zauren tattaunawar na fadar Shugaban kasa ta ASO ROCK dake Abuja.

Shugaba Timubu ya bukaci kusoshin tsaron da su tabbatar suna yi aiki tare cikin hadin kai da kama-kama domin shawo kan kalubalen tsaro da ya dabaibaye kasar.

Shugaban wanda ya tabbatarwa hafsoshin cikakken goyon bayansa ya kuma tuna masu irin nauyin dake wuyansu, ya ce dole ne su kara jan damara wajen gudanar da ayyukansu

Mai baiwa Shugaban shawara kan sha'anin tsaro, Nuhu Ribadu ya ce a halin yanzu tsaron na dan inganta ya kuma kara da cewa za ayi aiki sosai don dorewar hakan.

Da ya ke wa manema labaru karin bayani a fadar shugaban kasa jim kadan bayan taron, Ribadu ya ce za ayi kokarin tsare Najeriya, duba da irin kwarewar hafsoshin da aka basu amanar hakan.

Mallam Nuhu Ribadu ya ce za su yi aiki wurjanjan don tabbatar da kare dukiya da rayukan ‘yan Najeriya a ko'ina cikin kasar

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG