ABUJA, NIGERIA - Da yake karin haske kan al'amarin, daraktan sadarwa na hedkwatar rundunar sojojin saman Najeriya Air Commodor Ayodele Famuyiwa ya ce kafin harin da rundunar ta kai ranar daya ga watan Janairun wannan shekara ta 2023, sun sami sahihan bayanai daga bangarori daban-daban da ke nuna ‘yan ta'adda na shirin kai farmaki a yankin.
Ya ce a lokacin kai farmakin, yankin na fama da aika-aikar ‘yan ta'adda kuma akwai wata makarantar sakandare a wajen da bayanan sirri suka nuna cewa ‘yan ta'addan sun tsara yadda za su sace dalibanta.
Air Commodore Famuyiwa ya ce saboda haka tun lokacin da aka sami bayanan anyi ta aikin bin diddigi don gano abinda ke faruwa, inda aka ga ‘yan ta'adda sun tattaru a gindin wata bishiya da yamma, can kuma aka ga wata mota ta kawo musu makamai, abin kenan da yasa aka kai farmakin.
Tun dai lokacin da suka kai harin kawo yanzu inji daraktan, ba a sake samun harin ta'addanci a yankin ba, abinda ke nuna kwalliya ta biya kudin sabulu.
Saurari cikakken rahoto daga Hassan Maina Kaina: