Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar Sojin Saman Najeriya Ta Nada Sabbin Kwamandoji


KWAMANDOJI DA HAFSOSHIN MAYAKAN SAMA
KWAMANDOJI DA HAFSOSHIN MAYAKAN SAMA

Rundunar sojojin saman Najeriya ta gudanar da wani garambawul a karon farko tun bayan nadin sabon babban hafsan mayakan saman kasar da shugaba Tinubu ya yi.

Babban hafsan hafsoshin saman, Air Vice Marshall Hassan Bala Abubakar ya amince da sauyawa manyan hafsoshi casa'in wuraren aiki a sassan kasar daban daban.

Wata sanarwa da kakakin rundunar sojin saman mai barin gado, Air Commodore AK Famuyiwa ya sanyawa hannu, ta ce sauyin ya shafi manyan hafsoshi a hedkwatar mayakan da kuma manyan kwamandojin rundunoni daban daban.

AVM Sayo Olatunde shi ne sabon hafsa mai kula da manufofi da tsare tsare da a ka tura hedkwatar tsaro.

Tsohon kakakin rundunar AVM Ibikunle Daramola zai ci gaba da rike mukamin hafsa mai kula da sadarwa, AVM Pious Oahimire sabon hafsa mai kula sashin gyare gyaren jiragen yaki, AVM Uche Nwagwu zai jagoranci bangaren kudi da kasafi.

AVM Idi Sani shi ne sabon hafsa mai kula da sha'anin mulki, AVM Michael Onyebashi a ka nada sabon hafsa mai kula da ingancin aiki, AVM Anthony Ekpe zai ci gaba da rike hafsa mai kula da sashin lafiya.

Bugu da kari an kuma nada sabbin kwamandoji daban daban na sojin saman dake jihohin Kaduna, Lagos, Benue da kuma birnin Abuja.

AVM Adeniyi Amesinlola yanzu shi ne sabon kwamandan cibiyar sake tsugunar da sojoji dake Oshodi a Lagos, AVM Hassan Alhaji shi ne kwamandan kwalejin hafsoshin soji dake Jaji, AVM Sani Rabe shi ne kwamandan cibiyar fasaha ta mayakan sama.

Sauran su ne AVM Adebayo Kehinde, wanda yanzu shi ne kwamandan kwalejin horas da dabarun yaki ta sojin sama da ke Markudi, AVM Esseng Efanga yanzu shi ne kwamandan cibiyar yakin sama, Air Commodore Edward Gwabket yanzu shi ne sabon kakakin rundunar sojin saman.

XS
SM
MD
LG