ABUJA, NIGERIA - Daraktan sashin kula da lafiyar jama'a na ma'aikatar, Dr. Sadik Abdulrahman ne ya bayyana haka inda ya ce tuni har cutar ta halaka wani yaro ‘dan shekaru hudu.
Dr. Sadik ya ce an yi gwaji akan wasu mutane takwas dake Tungan Wakilia bangaren DEI DEI dake wajen birnin inda aka sami tabbacin mutum daya na dauke da cutar.
Daraktan ya ce a watan Janairun wannan shekara gwamnatin Tarayya ta ankarar da barkewar cutar a jihohin Lagos, Kano da Ondo al'amarin kenan ma da ya sa hukumar kula da cututuka masu yaduwa wato NCDC ta ja hankalin baki dayan jihohin kasar da Abuja.
Dr. Sadik ya ce alamun cutar sun hada da zazzabi, yoyon majina, kumburin kafafu, tari da kuma kankarewar wuya da kuma haddasa mutuwa.
Saboda haka ya ce ma'aikatar raya babban birnin Tarayyar ta samar da isassun rigakafi a kanana da manyan cibiyoyin kiwon lafiya dari hudu da ke yankuna daban-daban na birnin.
Da yake karin haske kan cutar, shima babban Sakataren Hukumar kiwon lafiya a matakin farko na birnin tarayyar, Dr. Yahaya Isa Vatsa ya ce wadanda suka fi fuskantar barazanar kamuwa da cutar sune wadanda basu karbi ainihin rigakafin da ake bukata su karba ba.
Vatsa ya ce wasu karin alamun cutar sune kaikayin makogwaro, idanu su yi ja, da wahala wajen yin numfashi, yana mai cewa ana iya daukar cutar daga mutum zuwa mutum, ta hanyar atishawa ko tari da dai makamantan hakan.
Saboda haka, ma'aikatar raya babban birnin tarayyar ta shirya tsab don yin rigakafi a baki dayan kananan yara da ke a matakin shekaru goma sha hudu zuwa kasa a baki dayan birnin, kuma ta nemi a tuntubi cibiyoyin kiwon lafiya mafi kusa yayin da aka ga alamun cutar.