Bayan da ta dauki matakin janye tallafin man fetur a farkon wannan makon gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ce janye tallafin ba wani abu ne da zai tsaurara wa talakawa ba.
Mai magana da yawun gwamnatin kasar Mr. Dele Alake da ke jaddada hakan, ya ce har yanzu suna fatan lalubo bakin zaren cikin ruwan sanyi.
Amma a nata bangaren, kungiyar kwadago ta Najeriya NLC ta jaddada cewa ba gudu ba ja da baya, lallai sai an maida farashin man yadda yake a baya, kana a shiga tattaunawa daga nan kuma a yi nazarin baki dayan irin wahalhalun da janye tallafin zai jaza wa talakawa da nufin shirin yadda za a tunkaresu.
Da ya ke wa sashen Hausa na Muryar Amurka karin bayani, sakataren tsare-tsare na kungiyar NLC Comrade Nasir Kabir, ya ce ko kadan ba zasu amince da batun janye tallafin ba, ganin irin dimbin wahalhalun da hakan zai jawo.
Comrade Nasir ya ce rashin gyara matatun mai da gwamnati ta yi bayan tun da farko ta alkawarta yin hakan, da rashin yin tanadi don kula da walwalar 'yan kasa kafin daukar matakin shi ne babban kuskuren gwamnati.
Don haka ya ce suna nan sun ja daga a matsayinsu na 'yan kwadago sai sun ga abin da ya ture wa buzu nadi, saboda bai yiwuwa a kara jefa talaka cikin halin kaka-ni-kayi idan aka saida litar mai sama da Naira dari biyar a irin wannan hali na kuncin tattalin arziki.
Saurari rahoton cikin sauti: