Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tinubu Ya Shiga Tsakani A Rikicin DSS, EFCC


Hedkwatar Hukumar EFCC Da Ke Abuja
Hedkwatar Hukumar EFCC Da Ke Abuja

Tun da farko hukumar yaki da cin hanci da rashawa wato  EFCC, ta bayyana cewa ta kadu matuka da yadda jami'an hukumar DSS suka mamaye mata ofis da ke birnin Lagos inda suka tare kofar shiga hukumar da motoci masu sulke.

ABUJA, NIGERIA - Shugaba Tinubu ya umurci hukumar DSS da ta gaggauta barin ofishin hukumar EFCC da ke Ikoyi a jihar Lagos da ta mamaye shi a ranarTalata.

Shugaba Bola Tinubu ya shiga tsakani biyo bayan rikicin da ya barke tsakanin hukumar DSS da ta EFCC, bayan da jami'an DSS suka yi dirar mikiya ne a ofishin hukumar na EFCC, inda suka hana jami'an hukumar yaki da cin hancin shiga ofishin nasu inda aka rinka jin karar harbin bindigogi.

Kakakin Shugaban kasa Tunde Rahman cikin sanarwar da ya sanyawa hanu, ya ce shugaba Bola Tinubu ya baiwa hukumar DSS umarnin da ta janye daga ofishin na Efcc nan take.

EFCC
EFCC

Shugaban ya ce in akwai sa-in-sa tsakanin hukumomin biyu masu matukar muhimmanci to kamata ya yi su sasanta cikin lumana.

Kakakin hukumar EFCC na kasa cikin Wilson Uwajeren cikin wata sanarwar da ya aikawa manema labaru ya nuna cewa abin damuwa ne wannan mataki da DSS din ta dauka ganin sun shafe fiye da shekaru ashirin suna zaune tare da gudanar da ayyukansu a wannan gini.

EFCC ta ce Jami'an na hukumar DSS sun zo ofishinta ne dake lamba goma sha biyar akan titin Awolowo dake Ikoyin na jihar Lagos kuma suka hana jami'anta shiga harabar hukumar don gudanar da ayyukansu.

EFCC ta ce wannan mataki na hukumar DSS ya hana masu samun tsaiko wajen gudanar da ayyukansu da ma'aikatansu sama da su dari biyar kana an kuma kawo cikas a duk shari'un dake gaban kotu da ya kamata a saurara a ranar.

DSS
DSS

To amma hukumar DSS cikin martanin da ta mayar ta ce sam bata mamaye hukumar ta EFCC ba kamar yadda wasu jaridun Najeriya suka ruwaito. DSS ta ce sun dai je wurin da dama can mallakinsu ne kuma take gudanar da ayyukanta bisa doron kundin tsarin mulkin kasa.

DSS ta ce a zahirin gaskiya ba wani sa insa ko rudani akan wannan gini, ta ce kowa yanzu wannan wuri gininta ne, ta ce za ta yi mamaki in har wani ma tababar ko wannan gini mallakin waye?

Kakakin hukumar DSS na kasa Dr. Peter Afunyaya cikin wata sanarwa da ya aikawa Muryar Amurka, na cewa wannan gini fa mallakin tsohuwar hukumar National Security Organization ne wato NSO wanda wato hukumar SSS/DSS kenan a halin yanzu.

Hukumar DSS ta ce ita fa a iya saninta bata da matsala da hukumar EFCC akan ma ko menene kasancewar hukumomin biyu na aiki kafada da kafada cikin fahimtar juna da kwanciyar hankali.

XS
SM
MD
LG