Da yake jawabi yayin bikin karrama wasu daga cikin Hafsoshin Najeriya
da su ka rigamu gidan gaskiya yayin da su ke gumurzun kare Najeriya da
yan Najeriyar, Kwamandan Makarantar horas da Hafsoshin, Manjo Janar
Ibrahim Manu Yusuf, ya ce irin sadaukarwar da hafsoshin suka yi lallai za
a ci gaba da tunawa da su.
Janar Yusuf ya ce Jaruman Hafsoshi Ire Iren su Marigayi Laftanar Kanar
Abu Ali, Janar Zirkushu, Kanar DC Bako da dai sauransu an sanya ma wasu
muhimman gine ginen makarantar sunayensu, kana an kuma karrama wasu hafsoshin masu ritaya da su ma suka bada gudunmuwa wajen kare kasa.
Janar IM Yusuf ya ce an wallafa kasidu da ke bayanin irin jaruntar
Hafsoshin da suka rigamu gidan Gaskiya a wani mataki na zaburar da
dalibai suyi koyi da irin kazar kazar din yan mazan jiyan.
Tunda farko cikin jawabinsa Babban Hafsan Hafsoshin Rundunar Tsaron
Najeriya Janar Lucky Irabor ya ce Makarantar Horas da Hafsoshin wacce
ke ci gaba da zama dandalin Ilmi da ci gaba, na taka rawa wajen
kyankyashe hazikan hafsoshi.
Ya ce Makarantar na gudanar da bincik da ke taimakawa wajen samar da
hanyoyin da ke zama silar kara inganta tsaro. inda ke nanata irin
alakar dake akwai tsakanin tsaro da ci gaban kasa.
Yayin dai wannan biki, an kaddamar da wasu littatafai guda uku ciki
harda wanda ke bayani akan sha'anin tsaro da aka wallafa biyo bayan
wani babban taron kasa da kasa da makarantar ta shirya kan tsaro. kana
an kaddamar da ayyukan ci gaba da hukumar makarantar ta giggina.
Saurari rahoton Hassan Maina Kaina: